11
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ‘Yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna sun karɓi diyyar Naira miliyan 100 kafin sakin shugaban bankin kula da ayyukan noma a Nijeriya Alwan Hassan bayan ya kwashe kwanaki kusan 10 a hannunsu. Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a yanar gizo ta ce saɓanin faifan bidiyon da ‘yan bindigar suka gabatar cewar sun saki Hassan ne saboda yawan shekarun sa da kuma azumin watan Ramadan, wata majiya kusa da iyalan sa ta tabbatar da cewar sai da suka karɓi maƙudan kuɗi kafin sakin sa. Jaridar…