Tarihi

Ko kun san jihar Kano tana nan fiye da shekara 2000?

Ko kun san jihar Kano tana nan fiye da shekara 2000?

Daga MAHD M. MUHAMMAD Kano, gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, garin da a wannan shekara (2021) ya kai kimanin shekaru dubu biyu da goma sha bakwai (999 zuwa 2021). Gari ne da ya fara daga sansanin mafarauta a mafi shaharar ruwayoyi, har ya zama katafaren birni sannan ya rikiɗe ya koma masaurauta, sannan ya koma lardi, daga bisani kuma ya zama Jiha mafi yawan jama’a a duk faɗin Ƙasar Nijeriya. Wannan Jiha daga shekarar da aka ƙirƙire ta zuwa yau, ta samu jagorancin gwamnoni har goma sha shida daga shekarar haihuwarta 1967 zuwa 2021. Akwai gurare masu daɗaɗɗen tarihi a…
Read More
Yaushe Musulunci ya zo ƙasar Hausa?

Yaushe Musulunci ya zo ƙasar Hausa?

Daga INJINIYA AHMED MUHAMMED DAURA Fahimtar takamaiman lokacin da Musulunci ya fara zuwa ƙasar Hausa abu ne mawuyaci, saboda da farko dai babu wani tarihin da ya bayyana wata ƙungiya ko ƙabilar da ta kawo jihadi ko wani yaƙin musuluntar da Hausawa. Bisa ga wannan dalilin za a karɓi Musulunci ya fara zuwa ƙasar Hausa daga ɗaiɗaikun mutane, watau baƙin Musulmai. A nazarin baƙin Musulmai ya bada damar fahimtar abokan hulɗar ƙasar Hausa, wanda ya ƙunshi mashahuriyar cinikayyar Hausa da tsallaken hamada (Trans-Saharan Trade) kamar sassan Aljeriya da Libya na yanzu zuwa Rum da Turai, tsallaken tekun maditareniya. Hanyoyin sun…
Read More
Ɗanwaire gwanki sha bara (1924)

Ɗanwaire gwanki sha bara (1924)

Daga FATUHU MUSTAPHA Babu takamaiman ko wacce shekara aka haifi Ɗanwaire, sai dai an bayyana cewa asalin sunan sa Muhammadu. Iyayen sa da alama dai Fulani ne, kuma asalain sa shi da mutumin Kano ne. an haife shi a garin Waire da ke ƙasar Bichi a yanzu. Babu kuma wani cikakken bayani akan ko wane irin nau’in Fulani ne. A taƙaice dai, asali da tasowar Ɗanwaire abu ne da har yau masana basu samu wani cikakken bayani a ka ba. Amma dai an fara jin ɗuriyar Ɗanwaire ne a zamanin sarkin Kano Bello1882 – 1893. Hakan na nuni da cewa…
Read More