10
Apr
Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Zimbabwe sun nuna ya zuwa ranar Alhamis da ta gabata, an samu ɗalibai 106 daga wasu makarantun ƙasar guda biyu da suka harbu da cutar korona a cikin yini guda. Sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa ɗalibai 51 sun kamu da cutar daga makarantar Sacred Heart GirlsHigh School da ke Esigodini, sannan ɗalibai 55 daga makarantar Umzingwane High School. Kawo yanzu, ƙasar mai yawan al'ummar da ya haura milyan 15, mutum 1,525 aka tabbatar cutar korona ta yi ajalinsu. Sai dai a daidai lokacin da aka sake buɗe makarantun ƙasar, tsoron cewa…