Kasashen Waje

Ƙulla dangantaka da Ƙasar Sin domin samun sakamakon moriyar juna cikin sauri

Ƙulla dangantaka da Ƙasar Sin domin samun sakamakon moriyar juna cikin sauri

Daga CMG HAUSA Ranar 21 ga watan Augusta, muhimmiyar rana ce ga shawarar Ziri D'Ɗaya da Hanya Daya. A wannan rana, jirgin kasan ƙasar Sin ya tashi daga tashar ƙasa da ƙasa ta Xi’an dake yammacin ƙasar, ya nufi birnin Hamburg na Jamus. Wanda ya zama karo na 10,000 da jirgin ƙasa na ƙasar Sin ya je Turai a bana. A kuma ranar ce, aka fara fitar da jiragen ƙasa masu sauri na ƙasar Sin a hukumance, inda aka tura jiragen ƙasa masu amfani da lantarki da jerin jiragen gwajin layin dogon Jakarta zuwa Bandung, daga tashar ruwa ta Qindao…
Read More
Sin ta bayyana kalaman jakadan Amurka a Sin a matsayin shaidar dake nuna tunani irin na danniya

Sin ta bayyana kalaman jakadan Amurka a Sin a matsayin shaidar dake nuna tunani irin na danniya

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, ya ce kalaman da jakadan Amurka a Sin Nicholas Burns ya yi a lokacin wata zantawa da kafar watsa labarai ta CNN a kwanan nan, na nuni ga irin tunani na danniya da Amurka ke da shi. Jami’in na Sin ya ce, yayin zantawar Burns da kafar ta CNN, ya tabo batun ziyarar kakakin majalissar wakilan Amurka a yankin Taiwan, inda ya sauya fari zuwa baki, yana mai cewa an zuzuta lamarin fiye da kima. Ƙasar Sin ta gabatar da kakkausan ƙorafi ga Amurka a lokuta daban-daban, don gane…
Read More
Amurka mai satar mai daga Ƙasar Sham

Amurka mai satar mai daga Ƙasar Sham

Daga MINA Abokai, kwanan baya an bankado wasu ayarin motocin dakon mai na sojin Amurka sunafitar da man da suka sata daga ƙasar Sham zuwa sansaninsu dake Iraƙi ta wata hanya da ta hada ƙasar Sham da Iraƙi. Tun daga shekarar 2015, Amurka ta fara aikata irin wannan laifi,awatan Agustan da muke ciki kaɗai, Amurka ta aikata irin wannan abin kunya na satar mai da fitar da shi zuwa Iraƙi har a ƙalla sau 6. Yayin da fararen hula a birnin Damascus babban birnin ƙasar, ke dogayen layi don sayen man. “Duniya a zanen MINA” na zana wani hoto game…
Read More
Sin da Nijeriya sun sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitocinsu

Sin da Nijeriya sun sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitocinsu

Daga CMG HAUSA Jakadan ƙasar Sin dake tarayyar Najeriya Cui Jainchun ya gana da ministan kiwon lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, inda suka sa hannu kan takardar kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin asibitoci na hukumar lafiya ta ƙasar Sin da ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya. Sun kuma yi musanyar ra’ayi kan yadda sassan biyu za su kara ƙarfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a ɓangaren kiwon lafiya. Yayin ganawar da suka yi a Abuja a ranar 19 ga wata, jakada Cui ya bayyana cewa, asibitin al’umma ta jami’ar Peking da asibiti jami’ar Abuja, za su hada gwiwa domin tabbatar da matsayar…
Read More
Masanin Nijeriya: Sin aminiyar ƙasashen Afirka ce a kodayaushe

Masanin Nijeriya: Sin aminiyar ƙasashen Afirka ce a kodayaushe

Daga CMG HAUSA An kira taron masu shiga tsakani na tabbatar da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin taron tattauna haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka a ranar 18 ga wannan wata ta kafar bidiyo, inda shehun malami a cibiyar nazarin yadda ake daidaita rikici da wanzar da zaman lafiya ta tarayyar Najeriya, Oboshi Agyeno ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu na CMG cewa, sakamakon da aka cimma a jere yayin taron sun nuna cewa, a ko da yaushe ƙasar Sin ta kasance babbar aminiya ga ƙasashen Afirka. Oboshi Agyeno ya ƙara da…
Read More
Ana samun sakamako mai kyau a haɗin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka

Ana samun sakamako mai kyau a haɗin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka

Daga CMG HAUSA An gudanar da taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar haɗin gwiwar ƙasar Sin da ƙasashen Afirka (FOCAC) ta yanar gizo a ranar 18 ga wannan wata, inda ɓangarori daban daban suka cimma daidaito kan yadda za a gaggauta gina al'ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma a sabon zamani, da inganta haɗin gwiwar abokantaka a tsakanin ƙasashe masu tasowa, da kuma kiyaye amfanin dandalin tattaunawar na FOCAC. A shekarun baya-baya nan, bisa tsarin dandaloli irin su bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su…
Read More
Rokokin Long March na Ƙasar Sin sun kafa tarihi na harba kumbuna zuwa sararin samaniya

Rokokin Long March na Ƙasar Sin sun kafa tarihi na harba kumbuna zuwa sararin samaniya

Daga CMG HAUSA A safiyar yau ne, ƙasar Sin ta yi amfani da rokar Long March-2D wajen harba rukunin taurorin dan Adam zuwa sararin samaniya, wanda ya nuna nasarar da ƙasar ta cimma wajen amfani da rokar wajen harba kumbuna sau 103 a jere. Nasarorin da aka cimma a baya wajen amfani da rokar ta Long March a jere shi ne 102, wanda aka fara cimmawa daga shekara 1996 zuwa ta 2011. Tun daga ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2020, rukunin rokar Long March na ƙasar Sin, ya cimma nasarori 103 a jere a cikin watanni 27 kacal, inda…
Read More
Ƙasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin gina intanet a cikin shekaru 10 da suka gabata

Ƙasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin gina intanet a cikin shekaru 10 da suka gabata

Daga CMG HAUSA A matsayinta na ƙasar dake kan gaba wajen yawan masu amfani da intanet a faɗin duniya, ƙasar Sin na kan hanyar sauyawa daga yawan adadi zuwa raya harkar intanet mai inganci. A cikin shekaru goma da suka gabata, ƙasar ta cimma manyan nasarori wajen gina tsarin tafiyar da yanar gizo mai cike da tsaro, sakamakon kyautatuwar ababen more rayuwa masu inganci, da ci gaban fasaha da bunkasar tattalin arziki na zamani. Tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2021, adadin masu amfani da yanar gizo a ƙasar Sin, ya karu daga miliyan 564 zuwa fiye da biliyan 1.03, abin…
Read More
Haɗin gwiwar Afirka da Sin na taimakawa raya duniya

Haɗin gwiwar Afirka da Sin na taimakawa raya duniya

Daga BELLO WANG Duniyarmu na fuskantar matsalolin da suka haɗa da yaƙe-yaƙe, da rashin tsaro, da koma bayan tattalin arziki, da ƙarancin abinci, da annoba. Wannan yanayi ya sa ake buƙatar wani mataki da zai taimaka wajen sauƙaƙa yanayin da ake ciki da raya duniyarmu.To ko haɗin gwiwar ƙasashen Afirka da ƙasar Sin, zai iya biyan bukatunmu a wannan fanni? An gudanar da taron ƙolin masu tsara aiwatar da ayyukan da suka biyo bayan taron ministoci na 8, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)  ta kafar bidiyo jiya, inda manyan jami'an ɓangarorin Afirka da Sin, suka…
Read More
Ana baje kolin mutum-mutumin inji na ƙasa da ƙasa a Beijing

Ana baje kolin mutum-mutumin inji na ƙasa da ƙasa a Beijing

Daga CMG HAUSA An ƙaddamar da bikin baje-kolin ire-iren mutum-mutumin inji na ƙasa da ƙasa na shekara ta 2022 a jiya Alhamis a nan birnin Beijing, wanda ya samu halartar kamfanonin samar da mutum-mutumin inji, gami da cibiyoyin nazari sama da 130. Ana baje-kolin wasu mutum-mutumin inji sama da 500 a bikin bana, kana za a ɓullo da wasu sabbin nau’o’in mutum-mutumin inji fiye da 30 a wajen bikin, al’amarin da zai shaida nasarorin ƙirƙire-ƙirƙire, da fasahohin zamani a fannin mutum-mutumin inji. “Cibiyoyin da suke nuna goyon-baya ga taron mutum-mutumin inji a bana sun dara na shekarun baya,” in ji…
Read More