04
Jul
Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja A Juma'ar da ta gabata wata ƙungiyar Musulmi daga yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya ta ƙaddamar da Alƙur’anin da ta fassara zuwa harshen Ibo. Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ta 'Ibo Muslims D’awah Group', Malam Muhammad Muritala Chukuemeka ne ya bayyana hakan a ziyarar girmamawa da ƙungiyar ta kai wani kamfanin jarida da ke Abuja ranar Talata. “Yanzu haka muna da kwafi 500 na wannan fassarar Alƙur’ani, kuma mun aika guda 100 zuwa yankin Kudu maso Gabas domin ci gaba da aikin da’awa ga ’yan uwanmu ’yan ƙabilar Ibo, don haka ina kira ga…