09
Nov
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Raudhatu-Rasul Ayagi ta yi bikin bayar da kyaututtuka ga zakarun musabaƙar yabon Annabi Muhammad (SAW). Taron wanda shi ne karon na farko ya gudana ne a unguwar Gwauron Dutse, makarantar Hajara Buhari cikin birnin Kano. Bilyaminu Zakariyya Ayagi (Abulwarakat) shi ne shugaban ƙungiyar Raudha ya ce, sun shirya taron ne don zaburar da matasa yadda za a tsabtace yabon ma’aiki (SAW). Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero ya ce, ya yabawa wannan ƙungiya inda ya ce, "muna alfahari da samuwar irin wannan ƙungiyoyi da matasan cikin al'ummarmu ke yi don yadawa da qara…