09
Jan
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos Wata ƙungiya mai tallafa wa mata da ƙananan yara mai suna 'Motherhen Initiative' da ke Jos ta tallafa wa wasu yara almajirai su 50 da rigunan sanyi, takalman silifas, garin sabulun wanki da sabulun wanka. A wani ƙwarya-ƙwaryar taro da ƙungiyar ta gudanar a Unguwar Rikkos da ke garin Jos an faɗakar da almajiran waɗanda shekarun su ba su wuce 5 zuwa 12 ba, da su kasance masu tsaftace jikin su, suna kula da lafiyar jikinsu, musamman a wannan lokaci na hunturu. An kuma tunatar da su kan su nisanci yawace yawace a titi…