23
Nov
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Injiniya Abubakar Usman Ahmad, sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar masu sana'ar sayar da wayoyi a kasuwar titin Berut, ya bayyana cewa za su yi ƙoƙari wajen kawo sauye-sauye masu nagarta don bunƙasa ci gaban masu sana'ar sayar da wayoyi a kasuwar. Ya ce Allah ne ya ƙudurta shi zai samu nasara a zaɓen da aka yi, ba domin ya fi kowa ba, sai dai haka Allah ya so, don haka abokan kawo canji da suka yi takara tare su zo su ba shi haɗin kai da goyon baya, don haɗa hannu domin kawo ci gaba a…