23
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana ra'ayinsa akan salon kamun ludayin Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa. Masari ya bayyana ra'ayin na sa ne da yake jawabi a wurin wani taron liyafar cin abincin dare da Dattawan Jam'iyyar APC na jihar Katsina suka shirya domin karrama shi tare da yin addu'o'in samun nasara ga sabon Gwamnan da ta gudana a ɗakin taro na Paramount dake cikin birnin Katsina. A cewar Gwamna Masari, yana tare da Dikko Raɗɗa ɗari bisa ɗari kuma yana goyon bayan sauye-sauyen da yake yi domin inganta…