21
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A cigaba da daƙile ayyukan ta'addanci da ake fuskanta a lungu da saƙon ƙasar nan, Gwamnatin Nijeriya ta fara ƙoƙarin karɓe kadarorin waɗanda aka gano suna taimaka wa ko ɗaukar nauyin 'yan ta'adda ta hanyar amfani da kuɗaɗensu da shawarwarin su da dai sauransu don haɓaka ta'addanci a cikin ƙasar. Kamar yadda wasu gidajen jaridu suka rawaito, sun ce jami'an tsaro da sauran hukumomin ƙwararru a kan lamuran tsaro suna bibiyar kadarorin masu taimaka wa 'yan ta'adda da suka haɗa da kamfanoni da asusun ajiya na banki da kuma wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da…