08
Nov
Daga AMINA YUSUF ALI Wasu ƙasurguman shugabannin mayaƙan ISWAP, Mallam Ali Kwaya da Mallam Bukar Mainoka, sun haɗu da ajalinsu a hannun jami'an sojin Nijeriya a tafkin Chadi, ranar Asabar ɗin da ta gabata. Dubun Kwaya da Mainoka, waɗanda kuma manya ne a majalisar Shura ta ISWAP ta cika ne a lokacin da tawagar sojin sama ta 'Operation Hadin Kai' ta kai musu samame a garin Belowa. Mamatan biyu suna daga cikin ƙalilan ɗin mayaƙan ISWAP/Boko Haram da suka yi saura a boye a yankin Tumbuns, dake tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Abadam. Majiyarmu ta bayyana cewa, Sojojin Nijeriya sun…