29
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro a Jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Dr. Mohammed Bello Matawalle, ya kafa wasu sabbin dokoki har guda bawkai waɗanda kuma aka buƙaci al'ummar Zamfara su kiyaye su don taimaka wa gwamnatin jihar wajen cimma ƙudurinta na neman ganin bayan matsalolin tsaro a jihar. Cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ayuba N. Elkanah, ya fitar a ranar Lahadi ta zayyano waɗannan dokoki da suka haɗa da: Haramta cin kasuwannin mako-mako a faɗin jihar, haramta sayar da man fetur…