17
Feb
Daga BASHIR ISAH Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da 'yan bindiga sun sace ɗaliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara su 27 da ma'aikatar makarantar 3 da kuma wasu mutum 12, a garin Kagara cikin ƙaramar hukumar Rafi, jihar Neja. Bello ya tabbatar da faruwar haka ne ga manema labarai a ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala taron gaggawa da shugabannin tsaro a Minna, babban birnin jihar. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa 'yan bindigar sun shiga makarantar ne da misalin ƙarfe biyu na daren Laraba, inda suka kashe ɗalibi guda da sace…