18
Aug
A Talatar da ta gabata Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin korona samfurin AstraZeneca-Oxford guda 699,760 ta hannun COVAX a matsayin tallafi daga Ƙasar Birtaniya. Muƙaddashin jakadan Birtaniya a Nijeriya, Gill Atkinson tare da sauran manyan jami'ai ne suka ya yi tarayya da shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya, Dr Faisal Shuaib, wajen ƙaddamar da rigakafin. An ƙaddamar da maganin ne a ɗakin sanyi na ajiyar magunguna da ke daura da Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja. Rigakafin da Nijeriya ta karɓa ɗin wani ɓangare ne na rigakafin AstraZeneca ƙwaya milyan uku da…