09
Aug
Daga BASHIR ISAH Rundunar 'yan sanda a garin Keffi, jihar Nasarawa, ta cafke wasu matasa su shida masu fashi a intanet da aka fi sani da 'Yahoo Boys'. Sanarwar manema labarai da rundunar ta fitar wadda ta sami sa hannun mai magana da yawun 'yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, a madadin Kwamishin 'Yan Sandan Jihar, ta nuna biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu game da harkokin ɓatagarin ne sai jami'anta suka yi musu dirar mikiya a maɓuyarsu da ke G.R.A Keffi inda aka kamo su. DSP Ibrahim Muhammed Siraj shi ne jami'in da ya jagoranci dakarun da…