Labarai

Zamfara: Majalisa ta buƙaci Matawalle ya ɗauki mataki kan kuɗaɗen fansho

Zamfara: Majalisa ta buƙaci Matawalle ya ɗauki mataki kan kuɗaɗen fansho

Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta yi kira ga gwamnan jihar Bello Matawalle, da ya yi amfani da kuɗaɗen fansho Naira miliyan 500 da ke ɓoye a banki an rasa mai su wajen biyan ma'aikatan gwamnatin jihar da suka yi murabus haƙƙoƙinsu. Kazalika, majalisar ta buƙaci Gwamnan da ya nemi ganawa da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari'a, da kuma Babban Daraktan Hukumar Fansho ta Ƙasa domin tattauna yadda za a yi a biya ma'aikatan gwamnati a jihar abin da suka tara a can baya. A cewar Majalisar, "Wannan na daga cikin matsayar da ta cim…
Read More
Wataƙila cutar korona ta zama silar hana attajirai zuwa asibiti a ƙetare – Ume

Wataƙila cutar korona ta zama silar hana attajirai zuwa asibiti a ƙetare – Ume

Daga WAKILIN MU Wani Babban Lauyan Nijeriya kuma tsohon Babban Lauyan Jihar Imo, Chukwuma-Machukwu Ume ya ce, annobar korona ta ɗan taki wani matsayi na a yaba mata saboda tasirin da ta yi na kusa kawo ƙarshen bulaguron da wasu masu ƙumbar susa kan yi zuwa ƙasashen ƙetare don jinya. Ume ya ce, duba da yadda annobar ke ta yaɗuwa kamar wutar daji, hakan zai tilasta wa shugabannin siyasar Nijeriya gina manya asibitoci masu inganci kwatankwacin na sauran ƙasashen duniya da suka cigaba don kula da lafiyar al'umma. Waɗannan bayanai da Ume ya yi, suna ƙunshe ne cikin wata takarda…
Read More
Bauchi: Daliban makarantun kudi na iya neman gurbin karatu a makarantun gwamnati – Tilde

Bauchi: Daliban makarantun kudi na iya neman gurbin karatu a makarantun gwamnati – Tilde

Daga FATUHU MUSTAPHA Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta bayyana cewa, dalibai daga makarantun sakandare masu zaman kansu a jihar na iya neman gurbin karatu a makarantun gwamnatin jihar don shiga aji hudu (SS1). Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr. Aliyu I. Tilde ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar. A cewar kwamishinan, "Mun fahimci cewa iyaye kalilan ne da 'ya'yansu ke tafiya makarantun kudi ke da masaniyar cewa 'ya'yansu na da damar neman gurbin karatu a makarantun sakandaren gwamnatin jihar don shiga aji hudu ta hanyar amfani da sakamakonsu na BECE." Ya ci gaba…
Read More
Cutar Korona: Mutum 27 sun mutu a tsakanin sa’o’i 24 a Nijeriya

Cutar Korona: Mutum 27 sun mutu a tsakanin sa’o’i 24 a Nijeriya

Daga UMAR M. GOMBE Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa, an samu rasuwar mutum 27 cikin sa'o'i 24 a fadin kasa sakamakon Cutar Korona. Cibiyar ta sanar da hakan ne a shafinta na intanet a Juma'ar da ta gabata, inda ta ce kawo yanzu adadin wadanda suka mutu a fadin kasa a dalilin korona ya cilla zuwa mutum 1,557. Kazalika, NCDC ta sanar an samu karin mutum 1,114 da suka harbu da cutar ta korona a fadin kasa. Wanda a cewarta, "Ya zuwa yanzu mutum 128,674 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasa."…
Read More
NUJ ta yi rashi a Binuwai

NUJ ta yi rashi a Binuwai

Daga AISHA ASAS Allah Ya yi wa Shugabar Kungiyar 'Yan Jarida ta Jihar Benue, Comrade Victoria Asher, rasuwa. Asher ta rasu ne bayan da aka yi mata aiki ta haifi tagwaye. A sanarwar da sakataren NUJ na jihar, Moses Akarhan, ya fitar a wannan Asabar din, ta nuna Asher ta rasu ne da misalin karfe 8 na safiyar Asabar a asibitin FMC da ke Makurdi bayan da aka yi mata aiki. Tuni dai gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana kaduwarsa game da rasuwar. Kana ya yi fatan Allah ya bai wa iyalan marigayiyar juriya da danganar rashin.
Read More
Buhari ya jaddada bukatar hadin kan kasashen duniya wajen magance matsalolin duniya

Buhari ya jaddada bukatar hadin kan kasashen duniya wajen magance matsalolin duniya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jaddada bukatar da ke akwai na kasashen duniya su hada kawunansu su yaki annobar korona da sauran manyan matsalolin da suka addabi duniya. Buhari ya yi wannan furuci ne a fadarsa da ke Abuja, sa'ilin da yake karbar wasikun shaida daga sabbin jakadun Masar da Saudiyya da kuma Argentina a Nijeriya. A cewarsa, "Matsaloli iri guda ne ke ci wa kasashenmu tuwo a kwarya, ciki har da matsalar ta'addanci da tabarbarewar tsaro da sauyin yanayi da karuwar yawan al'umma da safarar mutane da rashawa da talauci da kuma safarar makamai manya da…
Read More
Bankwana: Buratai ya zayyano nasarorin da ya samu a tsakanin watanni 66

Bankwana: Buratai ya zayyano nasarorin da ya samu a tsakanin watanni 66

Daga AISHA ASAS Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Nijeriya, Lt. Gen. Tukur Yusuf Buratai ya ce, watanni 66 da ya shafe a matsayin shugaban rundunar sojoji abin a yaba ne. Ya ce, a zamaninsa fannin sojin kasar nan ya samu nasarori da daman gaske tsakanin 2015 zuwa Janairun 2021. Buratai ya fadi haka ne a jawabinsa na bankwana da ya yi yayin da yake mika ragamar aiki ga magajinsa Maj. Gen Ibrahim Attahiru, a Alhamis da ta gabata a Abuja. Kafin nada Attahiru a matsayin sabon shugaban sojojin Nijeriya da Shugaba Buhari a Talatar da ta gabata, Buratai ya kasance Babban…
Read More
Kiris ya rage Obasanjo ya yi mini ritaya daga aiki – Buratai

Kiris ya rage Obasanjo ya yi mini ritaya daga aiki – Buratai

Daga UMAR M. GOMBE Tsohon shugaban rundunar sojan Nijeriya, Lt. Gen. Tukur Buratai, ya bayyana cewa, kiris ya rage tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi masa ritaya daga aikin soja shekaru 21 da suka gabata. Ya ce, wannan ya faru ne a lokacin yana matsayin Manjo, tare da bayyana samun zarafin kaiwa matsayin 'Lieutenant General' da kuma Babban Hafsan Hafsoshi da ya yi a matsayin al'amari da ya shiga tarihi. Buratai, ya yi wadannan bayanan ne yayin da yake jawabin bankwana wajen mika ragamar aiki ga magajinsa Maj. Gen. Ibrahim Attahiru a babban ofishin sojoji da ke Abuja a…
Read More
Yadda mafarauci ya hallaka ahalinsa a Anambra

Yadda mafarauci ya hallaka ahalinsa a Anambra

Daga WAKILINMU Rahotanni daga yankin Amanuke a karamar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra, sun nuna wani mafarauci mai suna Uchechukwu Nweke, ya harbe matarsa Mrs Patricia da bindiga har lahira sannan ya banka wa gidansu wuta tare dansa Mr Obinna a ciki a bisa dalilan da ba a kai ga ganowa ba. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar CSP Haruna Muhammed ya tabbatar da aukuwar lamarin. Inda ya ce wanda ake zargi, ya aikata ta'asar ne a safiyar Alhamis, 28 ga Janairun 2021 kana daga bisani shi ma ya harbe kansa. CSP Muhammed ya ce, "'Yan bijilantin…
Read More
Inganta fannin lafiya shi ya fi muhimmanci ga Nijeriya bisa ga sayo rigakafin korona – Gates

Inganta fannin lafiya shi ya fi muhimmanci ga Nijeriya bisa ga sayo rigakafin korona – Gates

Daga FATUHU MUSTAPHA Hamshakin dan kasuwar nan na Kasar Amurka, Bill Gates, ya shawarci Nijeriya da ta karkatar da hankalinta zuwa ga inganta fannin lafiyarta maimakon kashe makudan kudade wajen sayo allurar rigakafin cutar korona. Gates ya ba da shawar ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai ta bidiyo a Talatar da ta gabata, inda ya yi kira ga Nijeriya da kada ta yi amfani da 'yan kudaden da ta ware don kula da fannin lafiyarta wajen sayen rigakafin COVID-19 mai tsadar gaske. Jaridar Manhaja ta kalato dan kasuwar na cewa, “Ina mai bada shawarar a bai wa…
Read More