Labarai

An bindige mai kaɗa ƙuri’a har lahira a rumfar zaɓe a Kogi

An bindige mai kaɗa ƙuri’a har lahira a rumfar zaɓe a Kogi

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga Jihar Kogi sun ce wani mai suna Umar Hassan ya rasa ransa bayan da aka harbe shi da bindiga a wajen zaɓen gwamna da ke gudana a jihar. MANHAJA ta kalato cewa, hakan ya auku ne ranar Asabar a rumfar zaɓe ta Agala Ogane a yankin Anyigba da ke Mazaɓar Sanatan Kogi ta Gabas. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu bayani a hukumance daga ɓangaren hukumomin tsaro kan batun. Wata majiya ta ce wasu da ake zargin 'yan barandan siyasa ne suka yi kisan. Mai magana da yawun Jam'iyyar APC na kwamitin yaƙin…
Read More
Sarkin Bauchi ya buƙaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayayyakin masarufi

Sarkin Bauchi ya buƙaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayayyakin masarufi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu a cikin makon da ya gabata ya kai ziyarar bazata ga wasu kasuwanni dake cikin birnin Bauchi da kewayenta domin ganewa kansa yadda 'yan kasuwa suke zuga farashin kayayyakin masarufi da zumar yi masu nasihar ta natsu. Yayin ziyarar ta bazata, Mai Martaba Sarkin ya kekkewaya kasuwanni da suka haɗa da wacce take Wuni, Muda Lawal da kuma ta Wajen Durum dake wajen gari, inda yayi hulɗoɗi da 'yan kasuwa domin ya jiyewa kansa ire-iren farashin kayayyakin masarufi, husasan ma masara, dawa, gero, alkama, da dai sauran…
Read More
An horar da ƙananan ‘yan kasuwa 102 dabarun inganta sana’o’i na zamani

An horar da ƙananan ‘yan kasuwa 102 dabarun inganta sana’o’i na zamani

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Ƙwararru kan harkokin kasuwancin da suka fito daga ɓangarori daban-daban sun shawarci ƴan kasuwa da masu ƙananan masana'antu su rungumi sabbin hanyoyin kasuwanci da fasahar sadarwa ta zamani, domin bunƙasa sana'o'insu. An yi wannan kiran ne a wajen taron da Dandalin Horarwa Kan Dabarun Sana'o'in Zamani na Mu Inganta Sana'armu wanda ya gudana a birnin Kano, da nufin wayar da kan ƙananan ƴan kasuwa, da samar da muhallin da za su baje-kolin sana'o'insu, don sabbin abokan hulɗa da ƙulla ƙawance tsakanin ƴan kasuwa da masu masana'antu. Taron Mu Inganta Sana'armu wanda shi ne irinsa na…
Read More
Gwamna Dauda Lawal ya ƙuduri aniyar kafa rundunar ‘yan bijilanti a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya ƙuduri aniyar kafa rundunar ‘yan bijilanti a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana cewa ta tayar da azama wajen yaƙi da 'yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a duk faɗin jihar, inda ta ce za ta samar da runduna ta musamman don tabbatar da tsaro a duk faɗin jihar.  Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da ya ke bayani game shirin da gwamnatin ta yi na zaƙulo wasu matasa daga Ƙananan Hukumomin jihar 14, waɗanda za su yi aikin samar da tsaro a Hukumar tsaron da gwamnatin za ta kafa mai suna 'Community Protection Guards (CPG),…
Read More
An yi jana’izar Sheikh Yusuf Ali a Kano

An yi jana’izar Sheikh Yusuf Ali a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kano, Sheikh Dokta Yusuf Ali rasuwa. Sheikh Dokta Yusuf wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya ya rasu ne a daren Lahadi bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 73. Ɗan marigayin, wanda ɗan siyasa ne, Muslihu Yusuf Ali ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa, an yi janaizar mahaifin nasa a ranar Litinin da Azahar a Masallacin Murtala da ke kusa da titin Gidan Zoo. Shehin malamin ya gudanar da rayuwarsa ta aikin gwamnati a matsayin alƙali, inda ya jagorancin kotunan Shari’ar Musulunci daban-daban…
Read More
Kogi, Imo, Bayelsa: Gobe za a gwada ‘imanin’ gwamnatin Tinubu

Kogi, Imo, Bayelsa: Gobe za a gwada ‘imanin’ gwamnatin Tinubu

•Zaɓen farko tun bayan kafuwar gwamnatinsa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kimanin masu kaɗa ƙuri’a miliyan 5.2 ne za su fito a ranar 11 ga Nuwamba, 2023 don zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi. Adedayo Akinwale, ya yi nazari kan matakin shirye-shiryen alƙalan zaɓe, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa. Yayin da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da Kogi da kuma Imo ke ƙara ƙaratowa a ranar 11 ga watan Nuwamba, jimillar mutane 5,409,438 da suka yi rajista a jihohin uku ke shirin zaɓar sabbin shugabannin zartarwa na jihohin uku. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa…
Read More
Gwamnan Oyo ya yi wa ma’aikata ƙarin Naira 25,000 a kan albashinsu

Gwamnan Oyo ya yi wa ma’aikata ƙarin Naira 25,000 a kan albashinsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa ma’aikatan jihar da ‘yan fansho za su riqa karɓar tallafin kuɗi na Naira 25,000 da kuma N15,000 duk wata na tsawon watanni shida har sai an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi. Ya kuma jaddada muhimmancin ma’aikata da al’ummar jihar wajen haɗa hannu da gwamnatin jihar domin bunƙasa tattalin arzikin jihar na tsawon lokaci. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan a ofishin gwamna, Sakatariya, Agodi a Ibadan. Ya yi nuni da cewa duk da cewa gwamnatinsa za ta…
Read More
Majalisar Dattijan Nijeriya na son a tsagaita wuta a Gaza

Majalisar Dattijan Nijeriya na son a tsagaita wuta a Gaza

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattijan Nijerya ta buqaci gwamnatin tarayyar ƙasar ta haɗa kai da wasu ƙasashe domin yin kira a tsagaita buɗe wuta a rikicin Isra’ila da Hamas. Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ne sojojin Isra'ila suke yin ruwan bama-bamai a Gaza, bayan mayaqan Hamas sun ƙaddamar da harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400 a Isra'ila, waɗanda mafi yawansu fararen hula ne, a cewar hukumomin Isra'ila. A cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas, adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya zarce mutum 10,000 ciki har da yara sama da 4,000. A wani ƙudiri…
Read More
’Yan bindiga sun yi wa masu taron mauludi yankan rago a Katsina

’Yan bindiga sun yi wa masu taron mauludi yankan rago a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun yi wa mutane yankan rago a wani taron Mauludi a yankin Kusa da ke Ƙaramar Hukumar Musawa a Jihar Katsina. ’Yan bindigar sun kashe mutumu 25, baya ga wasu 17 da suka tsallake rijiya da baya da aka kwantar a Babban Asibinin Musawa da kuma Asibitin Koyarwa na Katsina, a sakamkon raunukan da suka samu a harin. Manhaja ta gano mahalartar Mauludin sun zo taron ne daga ƙauyuka daban-daban na ƙanana hukumomin Musawa da kuma Matazu. Ɗaya daga cikinsu da aka kai Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina ya ce,…
Read More
Ranar Kimiyya Ta Duniya: UNESCO ta jaddada muhimmancin kimiyya ga cigaban duniya

Ranar Kimiyya Ta Duniya: UNESCO ta jaddada muhimmancin kimiyya ga cigaban duniya

Darakta Janar ta Hukumar Bunƙasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta jaddada tasirin da kimiyya ke da shi wajen samar da ingantacciyar duniya. Ta bayyana haka ne a cikin wani sakon da ta gabatar na bikin ranar kimiyya ta duniya don haɓaka zaman lafiya da ci gaba a ranar 10 ga Nuwamba, 2023. A cewarta, kimiyya ta taimaka wajen rage yaɗuwar cututtuka kamar COVID-19, baƙon dauro, da foliyo ta hanyar samar da allurar rigakafi. Haka kuma, ta ce UNESCO na tunawa da ranar Kimiyya ta Duniya ce don inganta zaman lafiya da ci gaba a kowace…
Read More