09
Apr
Daga BASHIR ISAH Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce an ga watan Ƙaramar Sallah a wasu jihohi biyar na ƙasar. Don haka, Talata take 1 ga Shawwal kuma ranar Ƙaramar Sallah a ƙasar. Sai dai, maƙwabciyar Nijar, wato Nijeriya da Saudiyya da sauransu, aun ce ba su ga wata ba, wanda hakan ya sa za su yi azumi 30 a ƙasashen sannan Laraba su yi Ƙaramar Sallah.