29
Jul
Daga BASHIR ABDULLAHI EL-BASH Tun farkon kafuwar Duniya har zuwa yau, a cikin kowane ƙarni, a ciikin kowace al'umma, a kowane zamani, Allah Ya na fito da wasu mata 'yan gwagwarmaya da su ke taimakon al'umma, Allah Ya bayyanar da Hajiya Maryam Shetty a wannan zamani namu. A fannin gwagwarmayar siyasa da ba da gudunmawa ga masu mulki, Hajiya Maryam Shetty ta na kamanceceniya da Sarauniya Raziya Shamsuddeen Iltutmish, wacce ta rasu shakaru 780 da suka gabata. Jarumar Mace ce wacce ta gaji mahaifinta a Birnin Delhi lokacin Indiya da Pakistan na haɗe, ta taimaki shugabancin Mahaifinta a sarari da…