21
May
A kwanaki kaɗan da suka gabata, wato ranar 16 ga Mayu, 2021, ne, Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya buga bulaguro zuwa Birnin Paris, babban birnin Ƙasar Faransa, inda Shugaban ƙasar ta Faransa, Emmanuel Macron, ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen Afrika a taron tattaunawa kan jikkatar da aka sha sakamakon ɓarkewar annobar Cutar Korona da kuma duba yiwuwar samun tallafi, musamman bisa irin bashin da ya yi wa ƙasashen na Afrika katutu, sannan kuma ya ke ci gaba da ƙaruwa. Sai dai kuma, a sanarwar da Fadar Shugaban Nijeriya da ke Abuja ta bayar mai ɗauke da sa hannun Babban Mai…