Ra’ayi

Me za mu yi kan tsadar abinci?

Me za mu yi kan tsadar abinci?

Daga MARHABA YUSUF ALI Wai jama'a bai kamata mu dage da maganar tsadar kayan abinci ba kamar yadda muka dage da maganar tsaro kuwa? Idan kai ka ci ka ƙoshi ba ka tuna wanda tun kafin rayuwar ta yi tsada da ƙyar suke samun abinda za su ci ma balle yanzu da komai ya tashi wani ma ya ninka? Magidanta da suka ajiye iyali a gida su wuni suna yawo a rana wani da ƙyar zai samu abin da zai ciyar da su sau ɗaya a rana. Wani jarin ma bai kai na dubu biyu ba, me ya samu? Me…
Read More
Gaskiyar magana game da rashin samun miji ko matar aure

Gaskiyar magana game da rashin samun miji ko matar aure

Daga AMINA YUSUF ALI Wannan maudu'i da za mu tattauna wannan mako, za mu duba yadda ake yawaitar samun samari da 'yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Ƙasashen Hausa cike suke da waɗannan matsaloli. Kuma kowa ka taɓa cikin waɗannan matasan sai ya ce ai ya rasa miji ko matar aure ne. Wasu lokutan ma har a kafafen sadarwa ko dandalin sada zumunta na yanar gizo daban-daban za ka ga an ba da cigiyar mutum yana neman matar aure iri kaza, ko mai kama kaza. Haka su ma matan sukan ɓoye sunansu na ainahi su tallata kansu a waɗancan kafafen…
Read More
Faruk Lawan: Ina aka kwana kan babban batun?

Faruk Lawan: Ina aka kwana kan babban batun?

A tsakiyar makon nan ne wata Babbar Kotu a Abuja ta yanke wa fitaccen tsohon ɗan Majalisar Wakilai na Tarayyar Nijeriya, Hon. Faruk Lawan, hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bayan da ta ce kama shi da laifin amsar na goro daga hannun wani babban attajiri kuma ƙasurgumin ɗan kasuwa a ƙasar, wato Mista Femi Otedola a shekara ta 2012 lokacin da Lawan ]in ke shugabantar Kwamitin Bincike kan Badaƙalar Tallafin Man Fetur. A yayin da ta ke yanke hukuncin, alaƙalin kotun, Mai Shari’a Angela Otaluka, ta ce, Hon. Lawan ya kasa tabbatar wa da kotu iƙirarinsa na cewa,…
Read More
Bincike kafin aure a Ƙasar Hausa: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

Bincike kafin aure a Ƙasar Hausa: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

Daga AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Masu karatu sannunku da bibiyar filinmu na zamantakewa wanda kuke karantawa kowanne mako a wannann jarida taku mai farin jini, Manhaja. A wannan mako za mu yi bayani a kan bincike kafin aure a ƙasar Hausa. Menene bincike kafin aure? Bincike wani abu ne da magabatan yaro ko yarinya da suka shirya yin aure suke yi kafin a kai ga amincewa da auren nasu. Iyaye kan himmatu wajen bincike don tabbatar da wanda yake zuwa wajen yarinyarsu nagartacce ne ko akasin haka. Yayin da su ma iyayen yaro ba a bar su a baya…
Read More
Ko Boko Haram ta yi sabon shugaba ne?

Ko Boko Haram ta yi sabon shugaba ne?

Daga BARISTA BULAMA BUKARTI A jiya ne dai wani sabon bidiyo da ya ke cire dukkan shakku game da mutuwar Shekau ya bayyana. Wannan gajeren bidiyon ya ɗauko hoton mayaƙan ƙungiyar Boko Haram na ɓangaren tsohon shugabanta Abubakar Shekau. Inda suke ƙara tabbatar da mutuwar tsohon shugaban nasu. Kakakin nasu mai suna Bakura Shalaba, ya bayyana tare da mayaƙa fiye da goma suna rufa masa baya. Inda ya yi addu'ar neman rahmar Allah ga Marigayi Shekau. Tare da kira ga 'yan'uwan sa masu riƙe da makamai da kada su bari abinda ya faru ya kashe musu gwiwa. Haka zalika, ya yi…
Read More
Ranar Dimukraɗiyya: Gwamnati na murna wasu na zanga-zanga

Ranar Dimukraɗiyya: Gwamnati na murna wasu na zanga-zanga

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne Nijeriya ta yi bikin cika shekara 22 da komawar ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya, inda mahukunta da `yan ƙasa suke ƙididdigar nasarori da kuma tarin ƙalubalen da ƙasar ta fuskanta da kuma wanda take kan fuskanta. Wannan shi ne karon farko da ake bikin a wannan rana tun bayan sauya ranar bikin daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni da hukumomin ƙasar suka yi a shekarar da ta gabata, don tunawa da zaɓen MKO Abiola; Zaɓen da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda a lokacin mutane…
Read More
Yadda magidanci ke ƙara rura wutar kishi a gidansa

Yadda magidanci ke ƙara rura wutar kishi a gidansa

Daga AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Sannunku da jimirin bibiyar filinku na 'Zamantakewa', wanda yake zuwar muku kowanne mako daga jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata mun yi magana a kan yadda rashin tausayi ya yawaita a tsakanin kishiyoyi, haka a makon da ya gabace shi, shi ma mun yi magana a kan yadda namiji zai ɗauki matakan samar da zaman lafiya a lokacin da zai ƙara aure. A wannan makon kuma, mun zo mu ku da bayani a kan yadda magidanta ke ƙara assasa kishi a tsakanin matansu.…
Read More
Mutum da gaɓɓansa (2)

Mutum da gaɓɓansa (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI 'Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin  ɗan-Adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda ƙirar jikinku ta ke da kuma yadda take aiki.  Mu je kogon ƙugu:Akwai abubuwa masu matuƙar muhimmanci a ciki irinsu mahaifa, bututun wucewar maniyyi, hanyoyin jini, da sauransu. Idan muka ɗauki mahaifa misali, za mu shafe tsawon lokaci muna bayani akanta. Abubuwan da suka shafi mahaifa sun haɗa da yadda take ɗaukar ciki, yadda take samar da jinin haila da na biqi,…
Read More
Rikicin Tiwita: An bar jaki, ana dukan taiki

Rikicin Tiwita: An bar jaki, ana dukan taiki

A makon jiya ne, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya aike da wanikakkausan saƙo ga waɗanda suka addabi ƙasarsa da fitinar tsaro ta hanyar kashe rayuka, ɓarnata dukiya da kai wa ofisoshin gwamnati hare-hare. Shugaban yana mayar da martani ni kai-tsaye kan ƙungiyar ’yan ta’addar nan ta IPOB mai fafutukar kafa Ƙasar Biyafra, wacce a kwanakin nan ta ke kai hare-haren ta’addanci kan ofisoshin hukumar INEC da na ’yan sanda a yankin Kudu maso Gabas. Shugaba Buhari ya kuma yi furucin ne a Fadar Shugaban Ƙasa lokacin da Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya kai masa…
Read More
Murza gashin baki da Buhari ya yi

Murza gashin baki da Buhari ya yi

A yamma ranar 1 ga Yuni, 2021, Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya yi wani furuci ma jan hankalin da ya dace da buƙatar Nijeriya da ’yan Nijeriya, wanda kuma ba kasafai ake samun sa aikata irin waɗannan kalamai ba. A taƙaice ma dai, gwamnatinsa ba ta cika yin irinsu ko da da yawunsa ne tun bayan kafuwarta a watan Mayu na shekara ta 2015 zuwa yanzu a watan Yuni na shekara ta 2021. Da yawa suna alaƙanta hakan da kasancewar Shugaban Ƙasar dattijo, Hausa-Fulani, ɗan Arewa, gogagge da sauran ɗabi’u makamantan hakan, waɗanda su ne suke sanya ake kallon…
Read More