16
Nov
Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kamar da wasa aka fara sanya hotunan kayan sayarwa da sana'o'i a zaurukan sada zumunta, ana aikawa da wanda aka saya, bayan an biya kuɗin ta banki, a motocin haya ko ta hannun wasu amintattu, yanzu wannan hanyar tallata kasuwanci ta zama babbar harka da miliyoyin ’yan kasuwa maza da mata ke samun kuɗaɗe masu yawa da abin rufin asiri. Da dama daga cikin waɗanda suke wannan kasuwanci ko dillanci, basu da rumfa ko shago, a gida suke ajiye kayansu, sai an saya sannan su fitar da shi zuwa tasha. Wasu kuwa ma ba su…