26
Mar
Daga NAJEEB MAIGATARI Kwanakin baya tattaunawa ta haɗa ni da wani aboki na, sai yake ce mun ai ana sane aka ƙi samar da rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro (Malaria) duk da irin yanda kuwa cutar ta addabi musamman ƙananun yara da yanda ta ke kashe su. Har ya jefo mun wata tambaya; me yasa ba a damu da samar da rigakafin ‘Malaria’ ba, amma aka damu mutane da yi mu su rigakafin cutar shan inna (Poliomyelitis) duk da cewar yanzu ba a fama da ita? Maganar gaskiya shi ne a wancan lokacin ba ni da amsar tambayar shi, saboda…