02
Jul
Daga MU'AZU HARDAWA a Madina A ci gaba da ƙoƙarin ilimantar da mahajjata game da muhimmancin aikin Hajji kaɓaɓɓiya da take yi, Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta gargaɗi mahajjatan ƙasar da suka isa ƙasa mai tsarki don sauke farali kan su kasance masu lura da kuma bin doka yayin zamansu a Saudiyya. Babban limamin Hukumar 'Yan Sandan Najeriya, Sheikh Alhassan Yaakub, shi ne ya yi wannan gargaɗi a lokacin da yake gabatar da nasiha ga mahajjatan a birnin Madina. Malamin ya buƙaci alhazan su gode wa Allah bisa baiwar da Ya yi musu ta zama daga masu sauke faralin…