Addini

Sheikh Nuru Khalid zai soma limanci a wani sabon masallacin Abuja

Sheikh Nuru Khalid zai soma limanci a wani sabon masallacin Abuja

Daga BASHIR ISAH Fitaccen malamin nan na Abuja da ya rasa matsayinsa na limamin masallacin rukunin gidajen 'yan majalisar tarayya da ke Apo, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya ce an naɗa shi babban limamin sabon masallacin Juma'a da aka buɗe a bayan rukunin gidajen CBN da ke Abuja. Sheikh Khalid ya bayyana sabon naɗin nasa ne yayin zantawarsa da jaridar Vanguard ranar Litinin a Abuja, yana mai cewa Juma'a mai zuwa, 8 ga Afrilu zai soma jagorancin Sallar Juma'a a sabon Masallacin. Kwamitin Masallacin Apo ya tsige Sheikh Khalid daga limanci ne saboda huɗubar da ya yi a kan matsalar…
Read More
An yi jana’izar shugaban majalisar malamai na JIBWIS reshen Nasarawa

An yi jana’izar shugaban majalisar malamai na JIBWIS reshen Nasarawa

A yau Litinin aka yi jana'izar Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, HQ/Jos reshen jihar Nasarawa, Ustaz Surajo Alhaji Sabo Keffi tare da mutum biyun da Allah Ya karɓi rayuwarsu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a jiya Lahadi, wato Asst National Org. Sectatry, Malam Adam Damaturu da kuma matar Al-Hafiz Idris Isa Nasarawa. An yi jana'izar ne a garin Fataskum, Jihar Yobe a ƙarƙarshin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir. Yayin sallar janazar Marigayan sun rasu ne a kan hanyarsu ta zuwa wajen Tafsirin Ramadan. Da fatan Allah ya sa Aljanna ta kasance makomarsu.
Read More
JIBWIS ta yi babban rashi a jihar Nasarawa

JIBWIS ta yi babban rashi a jihar Nasarawa

Allah Ya yi wa shugaban Majalisar na JIBWIS mai hedikwata a Jos, Sheikh Sirajo Alhaji Sabo rasuwa. Malam ya cimma ajalinsa ne sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da su a kan hanyarsa ta zuwa garin Danaturu inda zai gabatar da Tafsirin Ramadan na wannan shekarar. Baya ga Sheikh Sirajo, ƙarin waɗanda suka rasu a haɗarin har da Malam Adam Muhammad Damaturu, Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa (F.A.G) da matar Alaramma Hafiz Idris Isa Lafiya mai jan baƙi. Bayanan JIBWIS reshen jihar Yobe sun nuna gobe Litinin za a yi jana'izar marigayan da misalin ƙarfe goma na safe a garin…
Read More
An dakatar da Sheikh Nura Khalid daga limanci saboda zazzafar huɗuba

An dakatar da Sheikh Nura Khalid daga limanci saboda zazzafar huɗuba

Daga WAKILINMU Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen 'yan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin, wato Shiekh Nuru Khalid kan huɗubarsa ta ranar Juma'a. Cikin huɗubarsa ta ranar Juma'ar da ta gabata, Sheikh Nura Khalid ya caccaki gwamnatin Buhari kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashen rayuka a Nijeriya. A cikin huɗubar tasa, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na ƙin fitowa zaɓe. "Sharaɗin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu…
Read More
Gobe Asabar 1 ga Ramadan 1443 – Sarkin Musulmi

Gobe Asabar 1 ga Ramadan 1443 – Sarkin Musulmi

Daga AMINU ALHUSSAINI AMANAWA a Sokoto Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bada sanarwar ganin jinjirin watan Ramadan na Shekarar 1443 a sassan ƙasar nan. Sarkin ya bayyana cewa, Sun samu rahoton ganin watan Ramadan daga shugabanni da kuma ƙungiyoyin addinin Musulunci, tare da tantacewar kwamitin duban wata n'a majalisar. Mai Martaba Sarkin Musulmi yayi amfani da wannan damar wajen kira ga al'ummar Musulmi da su dage da ibada, tare da aiki da koyarwar addinin Musulunci dama addu'ar samun zaman lafiya a Najeriya bakiɗaya.
Read More
An kammala musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa a Bauchi

An kammala musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa a Bauchi

Daga MU'AZU HARƊAWA a Bauchi An kammala gasar musabaƙar karatun Alƙu'ani ta ƙasa kashi na 36 da aka gudanar cikin kwanaki tara a jihar Bauchi, inda jihar Borno ta zo na farko, yayin da Zamfara na biyu. Gasar wacce aka fara gudanar da ita cikin shekarar 1986 a ƙarƙashin Jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato; Jihar Kano ce kan gaba wajen samun nasara mafi rinjaye a tsawon shekarun. Amma a bana Alaramma Abba Sanyinna Goni Muktar daga jihar Borno shi ne ya zo na farko, sai kuma Malama Haulatu Aminu Ishaq daga jihar Zamfara ta zo ta farko a mata.…
Read More
‘Yan Kano da Gombe sun lashe musabaƙar Ƙur’ani a Abuja

‘Yan Kano da Gombe sun lashe musabaƙar Ƙur’ani a Abuja

Daga BASHIR ISAH An kammala musabaƙar Ƙur'ani na 2022 wanda gidan talabijin ɗin Gaskiya TV ya shirya da aka gudanar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja. Gasar wadda aka kammala ta a ranar Alhamis da ta gabata, ita ce irin ta ta farko da aka taɓa samu wata hukuma ko cibiya mai zaman kanta ta gudanar a ƙasa. Alhaji Hamza Tanko wanda ɗan kasuwa ne kuma ɗan asalin ƙasar Ghana kuma ya shahara wajen hidimta wa al'umma da dukiyarsa, shi ne ya ɗauki nauyin gudanar da wannan musabaƙar karo na farko a Nijeriya. Inda ya bayyana cewa, soyayyarsa ga…
Read More
Ramadan 2022: A nemi jinjirin wata gobe Juma’a – NMSC

Ramadan 2022: A nemi jinjirin wata gobe Juma’a – NMSC

Kwamitin Neman Wata na Ƙasa (NMSC) na Majalisar Ƙoli na Harkokin Musuluncin Ƙasa (NSCIS), ya bada sanarwar al'ummar Musulmin Najeriya a nemi watan Ramadan gobe Juma'a idan Allah Ya kai mu. Kwamitin ya ce gobe Juma'a take 1 ga Afrilun 2022 wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban, 1443, wanda hakan ya zama ranar farko da ya kamata a nemi watan na Ramadan 1443. NMSC ya bada sanarwar ta hanyar wallafawa a shafinsa na facebook. Kwafin sanarwar Idan Allah Ya sa aka ga wata a goben, hakan na nufin al'ummar Nijeriya za su tashi da azumi Asabar mai zuwa…
Read More
Madarasatul Irshad Littahfizul Ƙur’an ta yaye ɗalibai sama da 30 a Legas

Madarasatul Irshad Littahfizul Ƙur’an ta yaye ɗalibai sama da 30 a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Makarantar Madarsatul Irshad Litfahfizul  Ƙur'an dake lamba 9, kan titin Olowolagba a babbar kasuwar ƙasa da ƙasa wadda aka fi sani da suna kasuwar Mile1 da ke Legas ta yaye ɗalibai yara maza da mata sama da talatin. Taron ya gudana ne a harabar makarantar firamari dake kan titin Maidan a ranar Lahadin ƙarshen makon jiya.  Babban sakataren kasuwar ta Mile 12, Alhaji Idiris Balarabe Kano shi ne ya wakilci babban shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Dallatun Egbaland Abeokuta) a wajen taron kuma shi ya jagoranci shuwagabannin ɓangarorin kasuwar a wajan taron. Tunda…
Read More
NAHCON ta ziyarci Hukumar Alhazan Jigawa don shirye-shiryen aikin hajjin 2022

NAHCON ta ziyarci Hukumar Alhazan Jigawa don shirye-shiryen aikin hajjin 2022

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Tawagar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ziyarci Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, domin ganin yadda ta ke gudanar da shirye-shiryenta kan aikin hajji na bana. Da yake jawabi a lokacin ziyarar, jagoran tawagar kuma babban daraktan duba ayyuka na hukumar aikin hajji ta ƙasa, Alhaji Usman Shamaki ya ce sun ziyarci hukumar alhazai ta jihar Jigawa ne domin duba kayayyakin aikin hukumar dangane da fara shirye-shiryen aikin hajjin na bana. Ya yaba da irin kayayyakin aiki na zamani da tawagar ta gani a hukumar jin daɗin alhazan ta jihar Jigawa.…
Read More