12
Apr
Daga WAKILINMU A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajjin bana, Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Kaduna ta ce kawo yanzu an samu yi wa maniyyata 2,837 allurar rigakafin cutar korona a jihar. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar Riƙon Ƙwarya ta Hukumar, Hannatu Zailani, a wata ganawa da ta yi da manema labarai, tana mai cewa an soma gudanar da shirin yi wa maniyyatan rigakafin ne tun ran 6 ga Afrilun da ake ciki. Hannatu ta ce daga cikin maniyyata sama da 4,000 da jihar ke da su a bana, mutum 2,837 ne suka je…