Daga AMINA YUSUF ALI
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya amince da soke lasisin da aka ba wasu bankunan ƙananan kasuwanci 132 da suke harkokinsu a Nijeriya.
Emefele ya amince da amshe lasisin a ranar Litinin ɗin da ta gabata, a cewar wani jawabi da CBN ɗin ya saki a ranar Talata.
A cewar jawabin, Bankin ya ƙaddamar da hukunci a kan ƙananan bankunan kasuwanci bankunan da ba sa yin biyayya ga ƙa’idojin CBN da kuma sharuɗɗan amfani da lasisin.
Daga cikin dalilan da ya sa bankin ya ƙwace lasisin, ya bayyana cewa ya ƙaddamar da wannan aikin ne, saboda bankunan ba sa gudanar irin kasuwancin da aka ba su lasisin amfanin wata shida saboda shi ba.
Bayan rashin cika sharuɗɗa kuma, an bayyana cewa, bankunan sun kasa yin biyayya ga haƙƙin da CBN ya ɗora musu bisa doron dokar Bankuna ta (BOFIA) 2020, Act No. 5. Ta kundin tsarin mulkin ƙasar nan.
Wasu daga cikin bankunan da aka ƙwace wa lasisin sun haɗa da:
- ATLAS MICROFINANCE BANK
- BLUEWHALES MICROFINANCE BANK
- EVEREST MICROFINANCE BANK
- IGANGAN MICROFINANCE BANK
- MAINSAIL MICROFINANCE BANK
- MERIT MICROFINANCE BANK
- MINNA MICROFINANCE BANK
- MUSHARAKA MICROFINANCE BANK
- NOPOV MICROFINANCE BANK
- OHON MICROFINANCE BANK
- PREMIUM MICROFINANCE BANK
- ROYAL MICROFINANCE BANK
- STATESMAN MICROFINANCE BANK
- SUISSE MICROFINANCE BANK
- VIBRANT MICROFINANCE BANK
- VIRTUE MICROFINANCE BANK
- ZAMARE MICROFINANCE BANK
- NORTH CAPITAL MICROFINANCE BANK
- CHIDERA MICROFINANCE BANK
- EXCELLENT MICROFINANCE BANK
- NI’IMA MICROFINANCE BANK
- COSMOPOLITAN MICROFINANCE BANK
- PROGRESSIVE LINK MICROFINANCE BANK
- TRUST ONE (FOMERLY DESMONARCHY)
- EKUOMBE MICROFINANCE BANK
- FIRST INDEX MICROFINANCE BANK
- OLA MICROFINANCE BANK
- ULI MICROFINANCE BANK
- VERDANT MICROFINANCE BANK
- AGULERI MICROFINANCE BANK LIMITED
Da sauransu.