CBN ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 16

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ba da sanarwar ƙarin kuɗin ruwa daga kashi 11.5 a bara zuwa kashi 16.5.

A ranar Talata Emefiele ya ba da sanarwar haka a Abuja.

Da ma dai CBN, ƙarƙashin kwamitinsa na dokar hada-hadar kuɗaɗe ya kaɗa ƙuri’ar neman ƙara kuɗin ruwan zuwa kashi 17.5.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *