CBN ya ƙaryata iƙirarin rage darajar Naira akan Dala

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Bankin Najeriya CBN ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya rage darajar Naira zuwa kusan Naira 630 akan dala.

Tun da farko dai rahoton faɗuwar darajar kuɗin ne ɗaya daga cikin jaridun ƙasar ta ruwaito.

Sai dai a wata sanarwa a ranar Alhamis, muƙaddashin shugaban sashen sadarwa na bankin, Dr Isa Abdulmumin, ya bayyana hakan a matsayin ƙarya.

“Rahoton labarai, wanda a tunanin jaridar ya keɓanta, cike yake da ƙarya da ɓatanci, wanda ke nuna yiwuwar jahilci da gangan game da yadda kasuwar canji ta Nijeriya ke aiki,” inji shi.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, don kauce wa shakku, an sayar da farashin canji a kasuwar  (I&E) a safiyar Alhamis 1 ga Yuni, 2023 a kan Naira 465 kowace dala kuma ya tsaya tsayin daka a daidai wannan farashin na wani lokaci.

Babban Bankin ya gargaɗi ‘yan Nijeriya da su yi watsi da iƙirarin gaba ɗayansa, domin hasashe ne da kuma aka ƙirƙire shi don haddasa firgici a kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *