Daga BASHIR ISAH
Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ba da umarnin bankuna su ci gaba da karɓa da kuma ba da tsoffin tarkadun kuɗi na N200 da N500 da N1000 har zuwa 31 ga Disamban 2023.
CBN ya amince da hakan ne domin cika umarnin Kotun Ƙoli biyo bayan hukuncin da kotun ta yanke ran 3 Maris inda ta buƙaci da a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin har zuwa ƙarshen wannan shekarar.
Muƙaddashin Daraktan Sadarwa na bankin, Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyna amincewar CBN na ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin a sanarwar da ya fitar ranar Litinin.
Wannan na zuwa ne kwanaki 10 bayan da Kotun Ƙoli ta tsawaita wa’adin amfani da tsofaffi kuɗin zuwa Disamban 2023.
“Domin cika umarnin kotu da biyayya ga Dokar Ƙasa kamar yadda aka san gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ita, CBN ya bai wa bankuna odar su yi biyayya ga hukuncin Kotun Ƙoli wanda aka yanke ran 3 ga Maris, 2023.
“Kazalika, CBN ya gana da kwamitin ‘yan banki inda ya ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin na N200 da N500 da N1000 tare da sabbin da aka sake wa fasali ya zuwa 31 ga Disamban 2023,” in ji sanarwar.