CBN ya bai wa DisCos bilyan N33.4 don aikin rarraba mita, inji NERC

Daga FATUHU MUSTAPHA

Kawo yanzu, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bai wa Kamfanonin Rarraba Lantarki (DisCos) kuɗi Naira bilyan N33.4 daga cikin bilyan N59.2 da aka ware musamman domin aikin raba mita ga ‘yan Nijeriya na Gwamnatin Tarayya, in ji Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC).

Shugaban NERC, Engr Sanusi Garba ne ya bayyana haka yayin wata ganawa tsakanin Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sha’anin Lantariki da jami’an NERC da kuma wakilan DisCos, kwanan nan a Abuja.

Garba ya ce shirin raba mitar wanda ake sa ran gidaje miliyan guda su ci moriyarsa a faɗin ƙasa tsakanin Oktoban 2020 da Afrilun 2021, ya zuwa 19 ga Maris, 2021 an cim ma kashi 13 ne kacal da aiwatarwa.

Ya ce, “Tuni aka miƙa wa kamfanonin mitoci guda 403,000 daga cikin mita milyan guda da aka shirya rabawa, amma mita 127,000 kacal DISCOS suka raba wanda hakan ya yi daidai da kashi 13 cikin 100 na aikin bakin ɗayansa.

“Tsawon lokacin da aka tsara na aikin na rukunin farko, gidaje milyan ɗaya ake sa ran a raba wa mita a tsakanin watanni shida, wato daga Otoba, 2020 zuwa Afrilu, 2021 wanda hakan zai taimaka wajen rage ƙibin da ake samu na milyan 6.5.”

Ya ci gaba da cewa, “Duk da dai daga cikin kuɗi Naira bilyan N59.2 da aka ware domin zartar da aikin raba mitar CBN ya bai wa DisCos bilyan N33.4 amma aikin raba mitar na tafiyar hawainiya.

“Sai dai bisa la’akari da kuɗaɗen da ke hannun DisCos a yanzu, ana kyautata zaton za a samu ci gaba wajen aikin rarraba mitocin a ‘yan makonni masu zuwa.”

Tuni dai Kwamitin Majalisar ƙarƙashin jagorancin Sanata Gabriel Suswan ya nuna rashin gamsuwarsa dangane da jinkirin da aka samu wajen aiwatar da aikin raba mitar yadda ya kamata duk da cewa CBN ya saki kuɗi bilyan N33.4 albarkacin aiki.

Daga bisani, kwamitin ya buƙaci NERC da DisCos su sake bayyana a gabansa ya zuwa ƙarshen watan gobe domin sanin ko an samu ci gaba wajen aikin rarraba mitocin kamar yadda suka bada tabbacin za su aikata.