CBN ya ci tarar bankuna huɗu saboda sun ƙi rufe asusun Kiroftokaransi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ci tarar bankunan kasuwanci huɗu a ƙasar saboda saɓa umarnin da ya bayar na haramta gudanar da hulɗa da kuɗin intanet na cryptocurrency.

Tun a watan Fabarairun 2021 ne CBN ya umarci bankunan da su rufe dukkan asusun da ke mu’amala da cryptocurrency.

Cikin wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Bloomberg ta ruwaito ranar Laraba, bankunan da aka ci tarar sun haɗa da Stanbic IBTC Bank, da Access Bank, da United Bank for Africa (UBA), da Fidelity Bank.

Rahoton ya ce an ci tarar Stanbic Bank Naira miliyan 200 saboda ya gaza rufe asusu biyu da ake zargin an yi amfani da su wajen hulɗar kuɗin cryptocurrency.

Kazalika, an ci tarar Access Bank Naira miliyan 500 saboda ya ƙi rufe asusun crypto, yayin da aka ci tarar UBA Naira miliyan 100. Sai kuma bankin Fidelity da aka ɗora wa tarar miliyan 14.