CBN ya samar da katin ATM na bai ɗaya

Daga BASHIR ISAH

A matsayin ɓangaren na ƙoƙarin da yake yi na inganta sha’anin hada-hadar kuɗi a ƙasar nan, Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya samar da katin cire kuɗi (ATM) na bai ɗaya.

CBN ya ce da wannan sabon katin na ATM, za a sadar da ko asusuwa nawa mutum ke da su da katin ta yadda za a iya amfani da katin wajen cire kuɗi a na’urorin ATM a bankuna daban-daban da sauransu.

Katin mai taken ‘1 BVN = 1 ATM CARD’ in ji CBN, zai yi aiki ne a tsakanin bankunan da ke mabobi a tsarin mu’amalar bankuna, wato ‘Nigeria Inter-Bank Settlement System (NIBSS)’.

Samuwar sabon katin na nufin daga yanzu babu buƙatar mutum ya riƙe sama da katin ATM ɗaya kafin cire kuɗi a bankunan da yake da ajiya.

Kuma hakan zai sa a dakatar da tsoffin katunan da aka saba amfani da su in ji Babban bankin.

CBN ya ce ana sa ran sabon katin ya fara aiki daga ranar Litinin, 16 ga Janairu, 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *