CBN ya umarci bankuna su fito aiki ranakun ƙarshen mako

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna da su ƙara kwanakin aikinsu zuwa Asabar da Lahadi.

CBN ya ce ya yanke hakan ne domin tabbatar da wadatar kuɗi a bankuna don amfanin jama’a.

Bankin ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a ta bakin Daraktansa, wato Isa AbdulMumin.

Sanarwar ta ce tuni CBN ya fara tura kuɗaɗe zuwa bankuna a sassan ƙasa baki ɗaya.

“CBN ya ba da umarnin bankuna su loda kuɗi a cikin na’urorin ATM, sannan su ci gaba da aiki har da ranakun karshen mako.

“Bankuna za su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi don biyan buƙatun kwastominsu.

“Shugaban CBN, Mr Godwin Emefiele, da kansa zai jagoranci tawagar jami’an da za su kewaya domin tabbatar da bankuna sun cika wannan unarni,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *