Daga BELLO A. BABAJI
Babban bankin Nijeriya, CBN ya umarci bankuna da su fitar wadatattun takardun kuɗi ga al’umma a ciki da kuma na’urorin ATM.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata takardar haɗaka daga Daraktan gudanarwar takardun kuɗaɗe na riƙon ƙwarya, Muhammed Olayemi da Daraktar gudanarwa ta reshe, Aisha Isa Olatinwo.
Lamarin ya biyo bayan halin ƙarancin takardun nairori da al’umma suke fama da shi a ƙasar.
CBN ya kuma yi kira ga al’umma da su kai ƙarar duk wani banki da aka san bai bayar da isassun takardun kuɗaɗe a ciki da ATM zuwa ga waɗanda ke da alhakin kula da hakan da kuma bin hanyoyin da suka dace.
Cikin hanyoyin akwai lambar waya da za ta kai zuwa ga babban bankin kai-tsaye da kuma adireshin imel tare da bada cikakken bayanai game da bankin da ya ƙi bin umarnin.