CBN ya yi barazanar takunkumi ga bankunan dake raba tsofaffin takardun kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sha alwashin hukunta bankunan da ke ci gaba da cika na’urorinsu na ATM da tsofaffin takardun kuɗi na Naira, a daidai lokacin da wa’adin cire kuɗaɗen ya gabato.

Daraktan Sashen Kula da Harkokin Shari’a na CBN, Kofo Salam-Alada, wanda ya bayyana haka a wani taron wayar da kan jama’a a ranar Laraba 18 ga watan Janairu, 2023, a Kasuwar Computer Village da ke Legas, ya ce bankin ƙoli ya riga ya sanya ido ga bankuna kan lamarin.

Daraktan wanda ya wakilci Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce babban bankin na da sabbin takardun kuɗi na Naira masu yawa da za a raba wa bankuna.

“A yau zan iya gaya muku cewa CBN a kullum tana fitar da sabbin takardun kuɗi. Kamar yadda muke magana, bankuna suna tare da CBN suna karɓar kuɗi.

A gaskiya muna roƙon bankuna da su zo su karɓi kuɗi daga babban bankin ƙasa. Muna da waɗannan sabbin takardun kuɗi na Naira a rumbun ajiyarmu, kuma muna roqon bankuna da su zo su karɓe su.

“Duk na’urorin ATM su loda sababbin kuɗin. Yayin da muke ba da bayanin kula, ya kamata mu sami damar samun sabbin bayanan. Idan na’urorin ATM ɗin ba sa rarrabawa, sabbin kuɗi ba za su gudana ba,” inji shi.

CBN ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar ƙarshe na wa’adin karɓar tsohon Naira 200, 500 da 1000.