CBN zai rufe asusun bankin da ba a haɗa su da BVN ba

Daga AMINA YUSUFU ALI

A halin yanzu Babban Bankin Nijeriya, CBN ya shirya tsaf don ganin ya rufe asususn bankunan da ba a haɗa musu BVN a jikinsu ba. Wannan wani mataki ne da suka ɗauka don ganin an rage zambar intanet a bankuna.

Blaise Ijebor, Daraktan sashen kula da tsautsayi na CBN shi ya yi yi wannan sanarwar a taron shan ruwa da aka gabatar a ranar alhamis ɗin da ta gabata.

Ijebor ya bayyana cewa, mazambatan intanet suna amfani da hanyoyi da dama wajen damfarar asusun da ba haɗa shi da BVN ba. Wanda yake sauƙaƙa musu zambar idan babu BVN ɗin.

A rahototon da aka gudanar a watan Afrilun da muke ciki, an rawaito daga shafin NIBSS cewa, asusun ajiya miliyan 57.01 ne kaɗai suke da rajistar BVN daga cikin jimlar asusu miliyan 191.4 da aka buɗe a bankunan da ke faɗin ƙasar nan. Kuma daga cikin miliyan 191. 4, guda ma miliyan 133.5 ne kacal suke aiki.

Ijebor ya bayyana irin muhimmancin da yake akwai na bankunan da su bi dokokin da sharuɗɗan da suka dace, su ma masu ajiyar su ɗauki matakan kare kai daga zambar intanet.

A cewar sa, a halin yanzu CBN yana aiki tare gwamnatin Nijeriya don tabbatar da gyara lamarin tare da taimakon ma’aikatan da suke taimakawa da rajistar BVN ɗin.

Kodayake, Ijebor bai ba da wa’adin ranar da za a fara rufe asusun duk wanda ba shi da BVN ɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *