CBN zai sauya ƙa’idojin kasuwar canji

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana cewa zai sauya ƙa’idoji na gudanar da kasuwar canji da suka haɗa da soke tsarin musayar canjin kuɗaɗe da dama da aiwatar da tsarin bai-ɗaya na musayar kuɗi da barin kasuwa ta yi halinta game da farashin canjin kuɗaɗe.

CBN ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Bankin ya ce manufar waannan matakan ita ce ƙara yawan kuɗin ruwa da daidaito, baya ga tasirin hakan da za a iya haifarwa nan da nan ga harkokin kuɗaɗen ƙasar.

CBN ya sanar da soke tsarin raba kasuwar musayar kuɗaɗen waje zuwa farashi daban-daban, kuma a yanzu za a kammala dukkan hada-hadar ta hanyar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki.

Kazalika, yanayin kasuwa ne zai tantance kuɗin musanya.

Tuni dai CBN ya sanar da bankunan kasuwanci da ‘yan kasuwa cewa, za su iya sayar da kuɗaɗen ƙasashen waje a farashin da kasuwa ta ƙayyade.

Babban Bankin zai kuma sake ɓullo da wani tsari na “saye da sayarwa”, wanda zai bai wa dukkan ‘yan kasuwar da suka cancanci shiga kasuwar canji a kan farashin canjin da suka ƙayyade.