Cece-kucen bayan babban zaɓen Nijeriya

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiyar magana cece-kucen bayan babban zaɓen Najeriya na 2023 ya sha bamban da sauran zaɓuka daga wanda a ka fara a 1999 bayan dogon mulkin soja da ya zo yayin da su ka kifar da gwamnatin marigayi Alhaji Shehu Shagari bayan babban zaɓen 1983.

Kafin na tsunduma gadan-dagan cikin rubutu zan ce babban bambancin shi ne na bambancin addini wanda ko haka ne ko ba haka ba ne siyasar Nijeriya ta wannan karo ta ɗauko bambancin addini ta fito da shi fili ya zama cikin abubuwan da a ka yi amfani da su wajen yakin neman zaɓe.

Shin addinin da gaske za a bi ko dai kawai masu amfani da bambancin don samun ƙuri’a ne su haye madafun iko daga nan su cigaba da hulɗa da sauran abokan su masu hannu da shuni ba tare da nuna bambanci ba?

ko ma dai yaya ba lalle ne waɗanda su ka fake da addinin sun ma damu da addinin. Ba mamaki ba ma ruhin addini a jikin su. Mu je ma ko akwai ruhin addini haƙiƙa in an zo rantsar da shugaba sai ya rantse da cewa zai kare tsarin mulkin ƙasa ne ba tare da ware wani ɓangare ko wasu mutane ya ce ba ’yan addinin sa ba ne ko ma ’yan ƙabilar sa ba ne ko ya ce ba su kaɗa ma sa ƙuri’a ba.

Yauwa zan dawo na ce a baya akwai bambancin kudanci da arewacin, ƙabilanci ko manyan ƙabilu da ƙanana da sauran su. Bambancin addinin na nan amma ba a kambama shi sai dai a kan iya amfana da shi. Ga talakawa na ƙasa can samun dan addinin su ya lashe zaɓe na sa su farin ciki ne a zuciya ko da kuwa wanda ke kan karagar ba ya taɓuka abun kirki ga ƙasa.

Kazalika in Musulmi ne da daɗi a gan shi da farar babbar riga ya zo sallar Juma’a a babban masallacin Abuja in an yi sa’a bayan idarwa ya gaisa da limamai da ladani sannan in ya fito waje ya dagawa talakawa hannu. Idan Kirista ne ranar Lahadi zai je babbar cibiyar mabiya addinin Kirista da ke ɗaura da babban bankin Nijeriya CBN ya yi ibadarsa babban malamin majami’a ya yi ma sa addu’a sauran mahalarta su yi ta murna cewa ɗan uwan su ne shugaban ƙasa.

A ’yan shekarun nan an ga irin hakan lokacin da marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ke mulki ya kan shigo masallaci ya yi sallar Juma’a hakanan a kan ga tsohon babban hafsan sojan ƙasa ma Janar Abdulrahman Dambazau ma ya kan zo masallacin.

Bayan mulkin shekaru biyu ’Yar’adua ya bar duniya sai mataimakinsa Goodluck Jonathan ya haye karaga inda ya kan halarci babbar majami’a ranar Lahadi kuma har an ga hoton da tsohon shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN Pastor Ayo Oritsejafor ya na shafa kan sa yayin da ya ke durƙushe.

Don ɗebe kewar ’Yar’adua mutane kan taru a babban masallacin Abuja a zamanin Jonathan don ganin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo in ya zo sallar Juma’a. An samu raguwar hakan a zamanin nan na shugaba Muhammadu Buhari don bai faye ko ma a ce ba ya sallar Juma’a a masallacin sai a masallacin fadar Aso Rock inda talakawa ba su da damar shiga don yanayin tsaron fadar.

Babban abun da ya fi zama a’ala a Nijeriya shi ne adalci. Daga kowane addini shugaba ya fito to ya yi adalci ya bar sauran ’yan ƙasa su yi addinin su ba tare da tsangwama ba. Wani abu ma da ya zama mai muhimmanci mai shugabantar Nijeriya ya mai da hankali a kan sa shi ne tabbatar da duk ’yan ƙasa ke iya zama a duk sashin kasa da gudanar da harkokin kasuwancin su ko lamuran su na yau da kullum ba tare da tsangwama ba.

A yau an wayi gari a ƙasar nan akwai inda wani ɗan ƙasa in ya je to sai yanda hali ya yi don zai iya rasa ran sa ma saboda bambancin addini ko ƙabilanci. Wasu ’yan ta’adda za su fito da manyan bindigogi su na farautar waɗanda su ke ganin ba ’yan uwan su ba ne. Mugun yanayin ya kai ma ga harbe jami’an tsaro da kai hari kan ofisoshin gwamnati.

Sannan a wani sashen kuma ba tabbas mutum ya tashi ko da rana ko da dare ya bi wasu manyan tituna face zuciyar sa ta na ɗar-ɗar wasu za sui ya tare hanya da bindigogi su harbe na harbewa su sace na sacewa su shige cikin daji. Lalle duk shugaban Nijeriya ba tare da duba daga kowane addini ya ke ba ya duba waɗannan manyan matsalolin don ɗaukar ƙwararan matakai wajen magance su.

Duk bambancin da ’yan ƙasa za su nuna a lokacin zave to sun fi samun lokaci bayan zaɓe don son samun rayuwa mai kyau fiye da tunanin dan addinin su ke kan madafun iko.

Masu iya magana kan ce ina ribar baɗi ba rai. Duk abun da ɗan ƙasa zai so samu ya na baya da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne. Ba wani cigaba mai ma’ana da za a iya cimma wa cikin yanayi na rudani da kiyaiya tsakanin ’yan ƙasa. Da zaman lafiya a ke iya yin ibada, sanin bambancin ƙabila ko ma ma yanki.

Lalle wannan shi ne babban abu da ya dace gwamnati ta maida hankali a kai samar da zaman lafiya ga ’yan ƙasa. Zaman lafiya kan tabbata ta hanyar adalci. A kan samu nasarar aiki da gyara ƙasa da adalci ko ba addini amma ba a iya samun nasarar cigaban ƙasa ko da addini matuƙar akwai zalunci.

A takaice ma in an duba addini na koyar da adalci ne ta hanyar yaƙi da zalunci. Don haka ko da an hau mulki bisa doron addini ko tasirin addini to ya dace a tabbatar da adalci don samun zaman lafiya mai ɗorewa. Wani abu kuma a al’adar rantsar da shugaba akwai rataya ma sa babban littafin addinin sa a lokacin da ya ke ɗaukar alƙawarin yin adalci ga kowa. Don haka ko ma me za a ce akwai amfanin addini a wajen rantsuwa don tsarin mulki ya ba da hurumin duk ɗan ƙasa ya yi addinin da ya kwanta ma sa a rai.

Ratayawa mai ɗaukar rantsuwa babban littafin sa na son karawa ɗaukar alƙawarin da zai yi qarfi ne don sanin cewa in ya ci amanar ’yan ƙasa to akwai hukunci a duniya ko a lahira. Zuwa yau dai an yi dacen duk waɗanda su ka dau rantsuwar mulkin Nijeriya wa imma Musulmi ne ko Kirista. Har yanzu ba a samu wanda ba shi da addini ko ɗan addinin gargajiya ya lashe zaɓe ba. Ba mu san me zai faru a lokacin rantsar da irin wannan ajin ba.

Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin na Nijeriya NBC ta ci tarar gidan talabijin na Channels naira miliyan 5 bisa kalaman da tashar ta yayata zantawa da mataimakin ɗan takarar jam’iyyar Leba Datti Baba Ahmed kan zaɓaɓɓen shugaba Bola Tinubu.

A shirin siyasa na gidan talabijin din Datti Ahmed ya ce ya saɓa wa tsarin mulki a rantsar da Tinubu saboda matsalolin da a ka samu a zaɓe.

A takarda zuwa Channels daga NBC mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar Balarabe Shehu Illela, hukumar ta ce kalaman na Baba Ahmed na iya tada fitina a ƙasa.

Don haka NBC ta ci tarar gidan talabijin ɗin naira miliyan 5 kuma a biya a mako biyu ko in lokacin ya wuce ba a biya ba kuɗin su ƙaru.

“In ba su biya ba za mu ɗauki wasu matakan ma kuma za mu iya kwace lasisin gidan talabijin ɗin don zaman lafiyar ƙasarmu ya fi kowa” in ji Balarabe Illela.

Ba wannan shi ne karo na farko da NBC ke cin tarar gidan talabijin na Channels da wasu kafafen rediyo a Nijeriya ba bisa nuna sun saɓa dokokin aiki na hukumar.

NBC ta ce ta sha zama da gidan talabijin ɗin kan irin waɗannan lamura don haka wannan matakin farko ne kan saɓa ƙa’idar.

Gwamnatin Nijeriya ta zargi peter obi da cin amanar ƙasa;

Gwamnatin Nijeriya ta zargi ɗan takarar jam’iyyar Leba Peter Obi da cin amanar ƙasa bisa kalaman san a zayyana zaɓen 2023 da cewa yaƙi ne na addini.

Ministan labaru Lai Muhammed ya zayyana zargin kan Obi da nuna cewa ɗan takarar na neman tada fitina ne a tsakanin ’yan Nijeriya su yi ta yaƙi da juna.

A nan Lai ya ce, maimakon Obi ya tafi kotu ko ya tsaya ga tanadin tsarin mulki wajen neman abun da ya ke ganin ba a yi ma sa daidai ba sai ya buge da haɗa fitinar addini.

An ji a wani faifan sauti Obi na magana da shugaban majami’ar WINNERS Pastor Oyedepo inda ya nemi taimakon sa wajen magana da mabiya su zaɓe shi kuma ya nuna zaɓen yaƙi ne na addini.

A martanin sa Peter Obi ya nuna takaicin yadda ya ce wasu manya a Nijeriya sun dage don cata ma sa suna da lankaya ma sa ɗabi’ar da ba ta sa ba ce.

Obi ya ce sam bai taba neman tada fitina a Nijeriya ko jawo faɗa a ƙasar ba don ya yi ikirarin ma shi mai son Nijeriya ne.

Kammalawa;

Babban abu dai Nijeriya ta Musulmi da Kirista ne da ma wanda ba shi da addini. Kauce wa tada fitina da fakewa da addini ko ƙabilanci ya fi zama a’ala ga jama’ar wannan ƙasa don ba alamar akwai mai ikon korar ɗan uwan sa daga ƙasar don tsananin kiyaiyar sa. In kuma wani ya yi yunƙurin yin hakan to ba mamaki shi kan sa ba zai kai labari ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *