Chadi ta kawo ƙarshen haɗin-gwiwa da sojojin Faransa

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙasar Chadi ta sanar da kawo ƙarshen haɗin-gwiwar sojojinta da na Faransa.

Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan da Ministan Harkokin Waje na Faransa, Jean-Noel Barrot ya ziyarci ƙasar.

Ministan Harkokin Waje na Chadi Abderaman Koulamallah ya wallafa hakan ta kafar Facebook.

Chadi ƙasa ce ta zama ginshiƙi ga kasancewar sojojin Faransa a Afirka.

A baya ne Faransa ta ɗauki matakin janye sojojinta daga ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar lamarin da ake ganin bai wa Chadin daɗi ba.

Ya ce lallai yanzu Chadi da kawo ƙarfi duk da cewa Faransa ta na da muhimmanci wajen ƙulla hulɗa da ita.