Chadi ta nemi goyon bayan ƙasashe wajen kan yaƙi da ta’addanci

Chadi ta buƙaci ƙasashe su ƙara ƙaimi wajen bada goyon baya wajen yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel. Kiran dai na zuwa ne bayan da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojojin ƙasar kusan 40 a wani hari da suka kai musu a cikin daren Lahadin da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin ƙasar Abderaman Koulamallah ya fitar, ta ce bayaga sojojin da aka kashe, wasu kimanin 20 sun samu raunuka.

Sao’i bayan kashe sojojin, shugaban ƙasar Mahamat Idriss Deby Itno, ya ƙaddamar da wani sintiri na bin diddigin maharan.

Ofishin jakadanci Faransa da ke Chadi, ya wallafa wata sanarwa da ke tabbatar da goyon bayansu ga ƙasar wajen yaƙi da ta’addancin da ta ke yi.

ƙasar ta Chadi dai ta bada hutun kwanaki uku da aka fara daga ranar Talata, tare da sassauto da tutoci da kuma hana gudanar da duk wani biki, don nuna jimami da kuma girmama sojojinta da ta rasa.