Chana ta ɓullo da sabon tsarin rage hayaƙi mai guba

Ƙasar Chana ta duƙufa wajen rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli ta hanyar inganta makamashi mai sabantuwa na zamani nan da shekara ta 2030 kamar yadda Majalisar Ministocin ƙasar ta sanar.

Sabon matakin tamkar nanata ƙudirin da Chana ke son cimma ne na daidaita ƙarfin iska da na rana zuwa gigawat 1,200 nan da shekaru 10 masu zuwa domin gina ƙarin cibiyoyin samar da wutar lantarki da nukiliya.

Waɗannan bayanai da Chana ta fitar na zuwa ne kwanaki ƙalilan gabanin fara babban taron sauyin yanayi a birnin Glasgow da aka shirya domin ƙarfafa wa ƙasashen duniya gwiwa wajen yaƙi da matsalar ɗumamar yanayi.

Manazarta kan sauyin yanayi sun jima suna sanya wa Chana ido wadda ke zama ƙasar da ta fi kowacce a duniya fitar da gurɓatacciyar isa.

Ana sa ran ƙasar ta Chana za ta sake gabatar da wasu alƙawura nan gaba dangane da rage ɗumamar yanayin kafin soma taron na birnin Glasgow.

A halin yanzu dai Chana na fama da matsalar ƙarancin lantarki, yayin da ta duƙufa wajen samar da gawayi domin ci gaba da rarraba lantarkin babu ƙaƙƙautawa a lokacin hunturu, yayin da Majalisar Ministocin ƙasar ke cewa, za su ƙara ƙaimi wajen gina sabuwar cibiyar samar da makamashi na zamani kuma mara gurɓata muhalli.