Daga AMINA YUSUF ALI
Bankin Exim na ƙasar Chana ya kore buƙatar Nijeriya na neman rancen Naira tiriliyan 10.12 (Wato Dalar Amurka $22,798,446,773). Wannan rance dai majalisar dokoki ta amince wa Buhari ya yi shi, a kwanakin baya.
Wannan rance dai an yi nufin a yi amfani da kuɗin wajen gudanar da aikin zamanantar da layin dogo/ gadar jirgin ƙasa ta Kano zuwa Kaduna.
Amma sakamakon kasawar Nijeriya wajen biyan basussukan, da kuma tasirin annobar COVID-19 a kan aikin, Bankin Exim na ƙasar Chana ya janye tallafinsa.
Haka, majalisar wakilai a zamanta na ranar Talata 28 ga Maris, 2023, ta amince da buƙatar gwamnatin Tarayya na buƙatar sake ranto Dalar Amurka $973,474,971.38 daga Chana Development Bank.
Shugaban kwamitin majalisar a kan dokoki da kasuwanci, Abubakar Fulata, shi ya gabatar da wannan ƙudiri ga zauren majalisar don samar da mafita ga wancan neman bashin da aka kore.