Chen Xu:Ya kamata a bincika tare da ɗaukar matakan doka kan waɗanda suke keta haƙƙoƙin yara ’yan asalin Afirka

Daga CMG HAUSA

Wakilin dindindin na ƙasar Sin a ofishin MƊD dake Geneva Chen Xu ya yi kira ga ƙasashe masu ruwa da tsaki, da su bincika, tare da ɗaukar matakin doka, kan sassan da suke keta haƙƙoƙin yara ’yan asalin Afirka, ta yadda yara ’yan asalin Afirka za su samu damar yin ingantacciyar rayuwa.

Chen Xu ya ce al’ummu ’yan asalin Afirka, da waɗanda suka fito daga nahiyar, sun shafe tsawon lokaci suna fuskantar muzgunawa ƙarƙashin laifukan wariyar launin fata da nuna kyama.

Jami’in na ƙasar Sin ya bayyana hakan ne, yayin taron tattaunawa tsakanin ƙwararru daga MƊD, dake ayyukan da suka shafi nazartar halin da al’ummu ’yan asalin Afirka ke ciki, da ’yan tawagar taron hukumar kare haƙƙin bil Adama ta MƊD karo na 51.

Chen Xu, ya ƙara da cewa, yara ’yan asalin Afirka na cikin yanayi na fuskantar barazana, da wahalhalu, da cutarwa mai tarin yawa.

Kana sau da yawa suna fama da ayyukan ƙarfi, da fatara, da barazanar harbin bindiga a makarantu da sauran haɗurra, yayin da kuma suke fuskantar keta haƙƙin su na bil aAdama, da ’yancin rayuwa.

Chen ya jaddada cewa, ƙasar Sin ta amince da shawarwarin da aka sanya cikin rahoton rukunin masu aikin na MƊD, tana kuma kira ga sassan ƙasa da ƙasa, da su rattaba hannu kan yarjejeniyar kare haƙƙin yara, su kuma sake yin cikakken nazari game da dokoki da manufofin ƙasashen su, su haramta duk wasu matakai, da manufofi dake da illa ga al’ummu masu asali daga Afirka, su kuma magance duk wani tsari na nuna wariyar launin fata.

Mai fassara: Saminu Alhassan