Chimaroke Nnamani ya bar PDP jim kaɗan bayan rasa kujerar Sanata a Enugu

Daga WAKILINMU

Tsohon gwamna a jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, ya tsallake ya bar jamiyyarsa ta PDP, bayan ya sha kaye a hannun jamiyyar LP a takarar Sanatan Enugu ta Gabas.

Zaɓaɓɓen Sanatan Enugun ta Gabas, Kevin Chukwu na jam’iyyar LP ya buga Nnamani ɗan takarar jamiyyar PDP da ƙasa da ƙuri’u 69,136, yayin da Nnamani, samu ƙuri’u 48,701.

An gudanar da zaɓen ne a Asabar ɗin da ta gabata biyo bayan kisan gillar da aka yi wa tsohon ɗan takarar sanatan na LP, Oyibo Chukwu, kwanaki uku kacal kafin ranar zaɓen ta ainahi wato 25 ga Fabrairu, 2023.

Nnamani, a wani jawabinsa ranar Litinin ya bayyana cewa, bayan tuntuvar mashawartansa da ‘yan mazaɓarsa, ya yanke shawarar barin jam’iyyar PDP sakamakon zazzafar rashin jituwar dake akwai tsakaninsa da shugabancin jamiyyar.

Sanatan mai-ci na Enugu ta Gabas, wanda ya bayyana goyon bayansa ƙarara ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, na jamiyyar APC Bola Ahmad Tinubu, an kore shi ne kafin babban zaɓen 2023 a kan zargin yi wa jamiyya zagon ƙasa.
Bayan jawabinsa na bayyana cewa ya bar PDP, Nnamani ya sake tabbatar da goyon bayansa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Tinubu, sannan ya yi alƙawarin cigaba da goya masa baya duk runtsi.

Ya ƙara da cewa, yana fata dukka gudunmowar da ya bayar ga mazaɓar tasa ta kasance tubalin da magajinsa mai hawa gado zai ɗora daga inda ya tsaya.

Daga ƙarshe ya gode wa ‘yan Nijeriya musamman ‘yan mazaɓarsa a kan su cigaba da jajircewa nan da shekaru masu zuwa.