China: An cafke mutum 80 masu haɗa jabun rigakafin cutar korona

Daga WAKILIN MU

Rahotanni daga ƙasar China sun nuna hukumomin ƙasar sun cafke wasu mutum 80 bisa zarginsu da harkar haɗa jabun maganin allurar rigakafin cutar korona.

Wani kamfanin dillancin labarai na ƙasar, Xinhua ya ruwaito cewa, ana zargin tun a watan Satumban da ya gabata waɗanda lamarin ya shafa suka soma harkar haɗa jabun rigakafin korona tare da sayar wa mutane da sunan magani mai inganci.

Hukumomin ƙasar sun ce, jabun rigakafin korona guda 3000 suka kama waɗanda aka yi aikin haɗawa a sassa daba-daban a ƙasar.

Kafin wannan lokaci, China ta samar da allurar rigakafin cutar korona da dama don amfanin ‘yan kasar.