China ta haramta wa ɗaliban firamare shiga aji da waya

Daga FATUHU MUSTAPHA

Kasar China ta sanar da ɗaukar matakin haramta wa ɗalibai ‘yan firame da na sakandare yin amfani da wayoyin salula a cikin aji.

China ta ce, ta ɗauki wannan mataki ne domin kare ɗaliban daga fitinar intanet da kuma ‘TV game’ da kan hana ɗalibai maida hankali kan karatu yadda ya kamata.

A wata takardar sanarwa da Ma’aikatar Ilimin ƙasar ta raba wa makarantu a Litinin da ta gabata, ma’aikatar ta ce daga yanzu ba a yarda ɗlibai a makarantun firamare da sakandare su riƙa amfani da wayoyi a aji ba.

Tana mai cewa, “Duk ɗalibin da ke da buƙatar hakan, to, wajibi ne ya sanar da hukumar makaranta a rubuce tare da samo izinin iyayensa.

“Idan hukuma ta amince da neman izinin da ɗalibi ya rubuto, ɗalibi zai iya zuwa makaranta da waya tare da miƙa ta ga hukumar makaranta don ajiya da zarar ya isa makaranta ta yadda ba za a shiga da ita cikin aji ba.”

Ma’aikatar ta ce, za ta duba ta samar da hanyoyin da ɗalibai za su riƙa ganawa da iyayensu yayin da suke makaranta a madadin amfani da waya.