Cibiyar koyar da Sinanci da aka yi wa gyaran fuska za ta ƙara inganta fahimta tsakanin Sin Da Nijeriya

Daga CMG Hausa

Gomman ɗalibai sanya da tufafi masu ban sha’awa ne suka buga ganguna tare da rera waƙe-waƙe domin murnar sake buɗe cibiyar koyar da harshen Sinanci da aka yi wa gyaran fuska, a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Sashen 18 na kamfanin gine-gine na China Railway ne ya yi wa cibiyar gyaran fuska.

An gina cibiyar ne a shekarar 2008, a makarantar ƙaramar sakandare ta yankin Garki Area 11 na birnin Abuja, da nufin kyautata fahimta tsakanin ƙasashen biyu tun daga matakin farko.

Alhassan Sule, shugaban hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta birnin tarayya Abuja, ya ce daddadiyar hulɗar da ke tsakanin Nijeriya da Sin, ta taimaka sosai ga hukumar ta samar da ilimin bai daya a birnin.

A cewarsa, masu kula da harkokin bayar da ilimi a yankuna, sun yaba matuƙa da gyara cibiyar da aka yi, kuma za su ci gaba da tabbatar da ana kula da ita da kayayyakin da aka sanya a ciki, ta yadda ɗalibai da malamai za su daɗe suna mora.

A nasa ɓangaren, jami’in ofishin jakadancin Sin a Nijeriya, Zhang Yi ya ce, ƙasar Sin za ta ci gaba da mara baya tare da bayar da muhimmanci ga aikin raya makarantu a ƙasar mafi yawan al’umma a Afrika.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha