Cikakken jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓen Kungiyar Lauyoyin Nijeriya na 2026

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An bayyana cikakken sakamakon zaɓen shugabannin ƙasa na ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) na shekarar 2026, bayan kammala zaɓe da kuma sanar da sakamakon da Kwamitin Gudanar da Zaɓen NBA (ECNBA) ya yi a ranar Lahadi.

Kamar yadda aka ruwaito a baya, Babbar Lauya mai Matsayin SAN, Misis Oyinkansola Badejo-Okusanya, ta zama shugabar NBA ta 33 bayan ta doke sauran manyan lauyoyi biyu da suka fafata da ita a zaɓen shugaban ƙungiyar.

Shugaban Kwamitin Gudanar da Zaɓen NBA (ECNBA), Aham Ejelam (SAN), ne ya sanar da sakamakon a hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja.

Badejo-Okusanya ta samu ƙuri’u 12,317, wanda ya kai kashi 47.18 cikin 100 na jimillar ƙuri’un da aka kaɗa. Ta kayar da babban abokin takararta, Lateef Omoyemi Akangbe (SAN), wanda ya samu ƙuri’u 7,934 (kashi 30.39 cikin 100), yayin da Olumuyiwa Akinboro (SAN) ya zo na uku da ƙuri’u 5,855 (kashi 22.43 cikin 100).

Da wannan nasara, Badejo-Okusanya za ta jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru biyu, daga 2026 zuwa 2028, inda ta zama mace ta biyu da ta taɓa shugabantar NBA bayan Dame Priscilla Kuye, wadda ta riƙe muƙamin tsakanin 1991 da 1992.

Bayanan da aka wallafa a shafin ECNBA tare da tabbatarwar da Aham Ejelam ya yi sun nuna cewa, daga cikin mambobi 82,172 da suka yi rajistar zaɓe, mutum 26,184 ne suka kaɗa ƙuri’unsu, adadin da ya kai kashi 31.86 cikin 100 na masu rajista.

A muƙamin Mataimakin Shugaban ƙungiya na Farko, Chief Oghenero Okoro ne ya yi nasara bayan samun ƙuri’u 11,024 (kashi 44.85 cikin 100), inda ya doke Luƙman Adekunle Laoye da Obajaja Onimisi Stephen.

A muƙamin Mataimakin Shugaban ƙungiya na Biyu, Egya Nuhu John ya zama zakara ba tare da hamayya ba, inda ya samu dukkan ƙuri’u 18,496 da aka kaɗa.

Haka kuma, Pepple Iniobong Irene ya zama Mataimakin Shugaban ƙungiya na Uku ba tare da hamayya ba, bayan samun ƙuri’u 19,200.

A zaɓen Sakatare Janar, Afam O. Okeke ne ya yi nasara da ƙuri’u 8,478 (kashi 33.58 cikin 100), inda ya kayar da Dr. Rapulu Ernest Nduka, Chidi Ezenwafor, Okey Leo Ohagba, Nnaebuka Onyebuchi Nwaeze da Barth Okoye-Aniche.

A muƙamin Mataimakin Sakatare Janar kuwa, Aghogho Gladys Okpomor ce ta lashe zaɓen da ƙuri’u 14,312 (kashi 56.76 cikin 100), inda ta doke Osato Uwagboe, Tijjani Magaji, Benjamin Emeka Enyiagu da Chiduabo Prince Henry Mamah.

Esther Ifeoma Jimoh ta zama Ma’ajin Kuɗi ba tare da hamayya ba bayan samun dukkan ƙuri’u 21,908. A zaɓen Sakataren Jin Daɗin Mambobi, Audrey Chinelo Ofoegbunam ce ta yi nasara da ƙuri’u 14,911 (kashi 60.43 cikin 100), inda ta kayar da Sir Oaikhena Osagie, Akinwunmi Laleye, Chiwendu Ugochukwu da Ernest Ezindu Uwanaka.

A muƙamin Sakataren Yaɗa Labarai, Dr. Prince I. Azubuike ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 14,686 (kashi 61.95 cikin 100), yayin da Lawrence Shegun Ayewa ya zo na biyu. Hadiza Nasir Ahmad ce ta yi nasara a zaɓen Mataimakiyar Sakataren Yaɗa Labarai da ƙuri’u 10,094 (kashi 40.83 cikin 100), inda ta doke Uwomano Anthony Junior Aki, Meti Monday Ukpeh da Lukman Oladimeji Jaiyeola.

A yankin Gabas, Chidi Betsy Nnaji ce ta zama wakiliyar yankin bayan samun ƙuri’u 10,497, inda ta doke Daniel Kip, Jane Omonor Apollos-James, Dr. Ehujuo Kingsley Chukwunonso, Assam Akpan Assam, Dr. Celestine Nwaokoma Nwankwo, Joy Obianuju Nnani da Arinze Celestine Chukwu.

A yankin Yamma kuwa, Rotimi Komolafe ne ya yi nasara da ƙuri’u 14,816 (kashi 43.17 cikin 100), inda ya kayar da Precious Ndidi Nwadimuya da Dhikrullah Adewale Balogun. A zaɓen wakilin yankin Arewa, Huwaila Muhammad Ibrahim ce ta zama zakara bayan samun ƙuri’u 13,327, inda ta doke Friday O. Enejor, Bulus Y. Atsen, Michael O. Olorunmola, Kadir Temim, Onimisi Friday Umar da Ledak D. Dafer.

By ukarofi