Cikin wasu ya ɗuri ruwa a Kebbi sakamakon sabuwar dokar fidda gwani

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Tun lokacin da bayanin majalisar dattawa ta saka hannu a lokacin zaɓen fidda gwani da za a yi labari ya mamaye kafafen yaɗa labarai na cewa cikin wasu ya ɗuri ruwa saboda suna ganin an ruguza duk wani coge da suka kitsa.

Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi Mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa a wata tattaunawa da ya yi da kafafen yaɗa labarai ya bayyana cewa, majalisar dattawan ta yi haka ne bisa ga la’akari da irin badaƙalar da ake yi wajen tsayar da ‘yan takara tun dawowa mulkin dimokuraɗiyya yau sama da shekaru ashirin inda ana amfani da waɗansu ‘yan tsirarrun mutane da ba su zarce dubu biyar ba wajen tsayar da ‘yan takara yanzu majalisa ta ga ya kamata a bai wa kowane ɗan jam’iyya damar taka rawa.

Yin haka zai hana duk wani coge ko amfani da kuɗi saboda yanzu jam’iyyar APC ta yi rajistar mutane milliyan arba’in, ashe ko ka ga ba wani ɗan siyasa da zai iya bibiyar kowa ya ba shi kuɗi don ya zaɓe a maimakon inda aka fito da duka isko ɗin nan dubu biyar ne inda za ka ga kafin a ɗauko su daga mazaɓunsu kowane sai an ba shi abinda zai bar wa iyalinsa, a ɗauka masa otel a saya masa abinci sannan kuma a sallame shi ka ga yanzu wannan duk ta kau.

A jihar Kebbi wakilinmu ya zagaya don jin yadda waɗansu ke kallon abin.
Habibu Adamu wani daga cikin jagororin matasan siyasar APC a jihar Kebbi ya bayyana wa wakilinmu da cewa, an sha su kuma mun warke Alhamdu Lillahi daman wannan lokacin shi ne suka daɗe suna jira wanda kowa zai sami ‘yanci a cikin jam’iyya saboda an daɗe ana yin son rai wajen tsayar da ‘yan takara a jihar Kebbi inda ga mutumin da mutane ke so amma sai a juya aƙalarsu da ƙarfin tsiya ta hanyar ko dai tursasawa ko kuma yin amfani da kuɗi wajen sayensu don su yi abinda waɗansu ke so musamman waɗanda ke riƙe da madafun iko.

Ya ci gaba da cewa, yanzu ko dai mutum ya gura halinsa da ma’amalarsa da al’umma ko kuma al’umma su ɗauki matakin da su ke so don ganin su ma sun kai ga abinda su ke so saboda yanzu an daina ɗauki ɗora da jeka na yi ka, kowa ya koma ya gyara tsakanin sa da mazaɓarsa.

Ya yaba wa majalisar dattawan bisa jajircewarta na ganin ba su watsa wa mutanen da suka zaɓe su ƙasa a ido ba.

Kashi kusan tamanin da biyar zuwa casa’in sun bayyana jin daɗinsu bisa ga wannan canjin da aka samu saboda a cewarsu an daɗe ana yin yadda aka ga dama wajen tsayar da ‘yan takara.

Hakazalika bayanai suna nuni da cewa waɗannan masu tsayawa ɗin ba ƙaramar rawa suka taka ba wajen jefa al’ummar ƙasar nan cikin bala’i ba ta hanyar tsayar wa da al’umma ‘yan takarar da ba su cancanta ba bisa ga dalilan barazana daga gwamnoni ko kuma ta hanyar karɓar waɗansu ‘yan kuɗaɗe da ba su taka ƙara suka ƙarya ba da ba su wuce cefanen sati ɗaya ba amma su jefa al’umma cikin wahalar shekaru huɗu ko kuma takwas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *